Search
Subscribe
Jaririyar kwana 3 da haihuwa ta bace a asibitin Filato

Jaririyar kwana 3 da haihuwa ta bace a asibitin Filato

Rahotanni na bayyana cewa, an samu bacewar wata jaririyar da aka haifa kwana uku a babban asibitin jihar Filato da ke Jos babban birnin. Asibitin dai ba su sallami mahaifiyar jaririyar ba aka dauke jaririyar.

Iyayen jaririyar da ta bace a asibitin, mahaifin mai suna Nwa God Chukwuebuka da mahaifiyar jaririyar Mary Chukwuebuka sun bayyanawa manema labarai cewa, an haifi jaririyar ne a ranar 28 ga Mayu 2019 sannan aka sace jaririyar a ranar 31 ga watan Mayu lokacin da wata likitar asibitin ke lura da jaririyar.

Mary, ta ce ta haifi ‘yarta ne da sassafe, kuma tana asibitin ne bayan haihuwarta saboda rashin jinin da ta samu bayan haihuwa, a yanzu haka ana yi mata karin jinin.

Wannan ita ce haihuwar Mary ta farko.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin