Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Jaruma Saratu Abubakar ta caccaki tsoffi masu lalata da  ’yan mata

Jaruma, Saratu Abubakar
Jaruma, Saratu Abubakar

Fitacciyar jaruma mai tasowa a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, Saratu Abubakar ta caccaki tsoffi masu kudi da suke ba ’yan mata kudi sannan su yi lalata da su.

Jarumar a cikin wani bidiyo mai tsawon minti daya da ta fitar ta kuma aiko wa Aminiya, ta caccaki mummunar dabi’ar da tsofaffi masu kudi suke yi na lalata ’yan mata ba tare da sun yi tunanin illar da hakan ke haifarwa ba.

ADVERTISEMENT

Ta ce, irin wadannan tsofaffin za ka same su sun ba nasu ’ya’yan tsaro inda ko fita za su yi sai tare da wani da zai rika sa musu ido, amma sai su zagaya ta bayan fage suna lalata ’ya’yan wadansu mutanen musamman na talakawa.

Ta ce, “Yarinya tana da shekara 17 kana lalata da ita, amma kai naka ’ya’yan ka kama ka yi musu takunkumi, idan za su fita sai da wani ko kuma ka sa musu ido, babu damar su wala, amma kai za ka iya daukar ’ya’yan mutane, ’ya’yan talakawa kana ba su Naira dubu 50 kana lalata da su. Wa kake yi wa wayo?”

ADVERTISEMENT

Jarumar ta bukaci masu irin wannan halin su tuba, sannan su rika taimakon ’yan mata ’ya’yan talakawa don su kama sana’a ba wai su rika tunanin sai sun yi lalata da su kafin su ba su kudi ba.

Ta ce, “Yanzu idan da gaske ne idan ka dauki Naira dubu 50 ko Naira dubu 100 ka ba yarinya kyauta, ba tare da ka yi wani abu da ita ba, sannan ka ce mata je ki nemi sana’a ina da irinki a gida, ka san irin ladan da za ka samu?

“Amma ina, sai dai ka rika lalata da su, wani har da cewa shi ba ya son manyan mata sai kananan yara ’yan shekara 17 ko 18. Haba ba ka tsoron Allah? Ba ka tsoron ranar da za ka mutu?,” inji ta.

Jarumar ta kuma shawarci ’yan mata da su guji amincewa da tsofaffi balle har ma su yarda a rika lalata da su, domin idan suka yi haka, to gobensu ba za ta zamo mai kyau ba.

Jaruma, Saratu Abubakar
Jaruma, Saratu Abubakar