Search
Subscribe
Jawaban Jonathan lami ne ba gishiri

Jawaban Jonathan lami ne ba gishiri

A yadda nake sauraren jawaban Shugaba Goodluck Jonathan, ina ganin hatta masoyansa na gani-kashe-ni sun amince da cewa jawaban nasa suna karancin hikima da fasaha da azanci, ba su da tasirin kama zuciyar mai sauraro. Da wuya mai sauraron jawaban nasa ya tsinci wasu kalmomin azanci, sai dai kawai a cika mutane da kalmomin ‘Sassanyar Iska’ ko ‘Ajandar Kawo Sauyi,’ wanda a gaskiyar lamari, babu inda za ka ga irin wannan ajanda a kasar nan.
Yana da wuya ka nuna wani mutum daya da zai ce maka zai iya tuna wani zance na azanci daga jawaban shugaban, domin kuwa jawaban nasa cunkushe suke da rashin balaga da rashin azanci. Bai iya zaben ingantattun kalmomin da suka dace ba, babu kwalliyar harshe, sannan kuma ga gazawarsa wajen iya zuba zance rairai, wanda haka kan yin masa tarnaki, ya hana jawaban nasa yin tasiri ga masu sauraro. Wannan ya sanya ma da wuya ka ga ana yanko irin tsararrun kalaman nan na fasaha daga jawabansa don nuni ko ishara, kamar yadda akan yi irin haka ga jawaban wasu shugabanni masu fasaha. Wannan shi ya sanya ma da wuya a ce ya iya gabatar da wani jawabi mai ma’ana kai tsaye daga kwakwalwarsa. Dalili ke nan ma yake da jami’an da ke rubutawa da tsara masa jawabai. Amma duk da haka, komai kyan jawabi, zai iya gurbacewa wajen karantawa. Haka ne ma ya sa na tuna da abin da marigayi Chinua Achebe ya ce, ‘kalmomi kamar gishiri ne da ke gyara miya.’
Idan za mu doka misali, mu dauki jawabin da shugaban ya gabatar a ranar ’yancin kai. Irin kwaba da rashin azancin da ke cikinsa ya sa nake ganin ya kamata ma a ce shugaban ya yi waje-rod da duk wanda ke da alhakin rubuta masa wannan jawabi. kunshiya da jigon jawabin nan sun yi hannun riga da zahirin abin da ke faruwa a kasar nan. Domin kuwa maimakon jawabin ya zama mai kanbama mutumincin shugaban, sai ma ya nuna shi a matsayin wani mutum marar alkibla. Masu rubuta masa jawabin suka banzatar da hakikanin al’amuran da ke faruwa a kasa, wanda haka ke sanyawa mutane su rika kallon shugaban tamkar wanda bai ma san abin da ke faruwa na zahiri a kasar da yake mulka ba. Wannan ya sanya ya kamata shugaban ya samu zarata kuma kwararrun marubuta jawabi, wadanda za su rika rubuta masa jawaban da za su rika kwankwasa zukata da jan hankalin al’umma. Wato irin jawaban da za su rika jan hankalin ’yan kasa domin su kasance masu kishin kasa da aikata abin da ya dace da ci gaban kasa.
A wannan jawabi na ranar daya ga Oktoba, lami ne ba gishiri, domin kuwa bai dauke da wani kalami na azanci da zai iya karfafa gwiwar ’yan kasa. Baya ga haka, wani cikas da ke kunshe da jawabin sun hada da tufka da warwara, wasu bayan nan nasa ba su dace da zahiri ba, sannan kuma ga shi dauke da misalan da ba na gaskiya ba a zahiri. Baya ga haka, hatta yanayin yadda shugaban ya karanta jawabin, yana ishara da cewa lallai abin takaici ne daga bangarensa, a ce wannan jawabi ne da ke fitowa daga Shugaban kasa.
Idan muka duba, mafi yawa daga kadarorin kasar nan a balbalce suke, harkar tsaro a lalace take, yadda ’yan ta’adda da ’yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane don amsar fansa suke cin karensu ba babbaka. A yau a kasar nan, wutar lantarki da ruwan sha sun zama sai gidan tajirai da masu rike da madafun iko. Idan ana batun harkar ilimi kuwa, tabarbarewar ta zama ta innanaha. Al’amuran walwala da jin dadin jama’a kuwa kusan babu su, babu tsaro sai tsoro da zullumi a ko’ina.
Duk da irin wadannan matsaloli da suka dabaibaye Najeriya, amma babu abin da masu rubuta wa Shugaban kasa sharhi suka ce game da haka sai: “Wadannan matsaloli suna nuna cewa wannan lokaci ne mafi tsanani ga kasarmu.”
Idan ka debe yadda aka tsiyata kasar nan, aka salwantar da dubban biliyoyi wajen tsare-tsaren da ba su da muhimmanci, yadda aka gaza kawo karshen sace-sacen albarkatun man fetur, kasar nan kuma tana ta kara zurfafa cikin duhun bashi, wanda ya yi mata katutu. Babu wani shiri mai kyau daga gwamnati, na yadda za ta rage rashin aikin yi da ya addabi al’ummar kasa.
Jawabin kuma ya kasa bayyana wa al’umma dalilin da ya sanya jami’o’in kasar nan suka kasance a rufe, balle a san hikimar yadda za a sasanta su dawo aiki. A takaice, jawabin dai ya zama lami kamar miyar da babu gishiri, domin kuwa Shugaban kasa ya kauce yin bayani game da matsalolin da ke addabar al’ummar kasa, sai ya bige da zagaye-zagaye. To, wannan wane irin jawabi ne kuma me za a kira shi?

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin