✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Abubuwa 4 da gwamnatin Najeriya ka iya bayani a kai

Fadar Shugaban Kasa ta ce Shugaba Muhammadu Buhari ba zai yi jawabi ba ga al’ummar kasa ranar Litinin a kan halin da ake ciki game…

Fadar Shugaban Kasa ta ce Shugaba Muhammadu Buhari ba zai yi jawabi ba ga al’ummar kasa ranar Litinin a kan halin da ake ciki game da yakin da Najeriya take yi da annobar coronavirus.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Twitter, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya ce da ma ba tsara cewa shugaban kasar zai yi jawabi ba, sabanin labaran da ke ta yawo a gari.

A maimakon haka, inji Mista Adesina, kwamitin kar-ta-kwana da shugaban kasa ya kafa don yaki da cutar zai fayyace matsayin gwamnatin a yayin jawabin da ya saba gudanarwa kowacce rana.

Ga hudu daga cikin abubuwan da ake hasashen bayanin zai tabo:

1. Yiwuwar janye dokar a Legas da Ogun da Abuja 

Ana sa rai kwamitin zai yi bayani a kan matakan da gwamnatin ke kokarin dauka don kara sassauta dokar kulle a Najeriya sannu-a-hankali, musamman a jihohin Lagos da Ogun da kuma Yankin Babban Birnin Tarayya.

Wannan yana kunshe ne a jawabin Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma shugaban kwamitin, Boss Mustapha, yayin da yake jawabi ga manema labarai a Fadar Shugaban Kasa, jim kadan bayan kwamitinsa ya kammala yin bayani ga shugaban kan halin da ake ciki a yaki da annobar.

2. Maganin Madagascar

A ranar Lahadin da ta gabata, gwamnatin tarayya ta tabbatar da karbo kasonta na maganin da kasar Madagascar ta sarrafa don yakar cutar.

Idan dai za a iya tunawa shugaban kasa ya ba da umurnin a yi cikakken bincike a kan sahihancin maganin kafin a amince a kuma fara amfani da shi a hukumance.

3. Matsayin gwamnatin tarayya a kan jihar Kano

Idan za a iya tunawa a ‘yan makonnin da suka gabata gwamnatin tarayya ta kakaba dokar kulle na tsawon makonni biyu a jihar Kano sakamakon yawan mace-macen da aka rika samu da wadansu ke alakantawa da cutar ta coronavirus.

To sai dai bayan karewar makonni biyun sai aka ji gwamnatin tarayyar ta ja bakinta ta yi shiru, sai daga bisani aka ji gwamnatin jihar ta kara mako daya.

Yanzu da wannan wa’adin na gwamnatin jihar zai kare a cikin wannan makon, ana sa rai gwamnatin tarayya ta yi bayani a kan jihar Kano.

4. Tallafin rage radadi

Hakazalika, ana sa ran gwamnatin za ta yi bayani a kan inda aka kwana zuwa yanzu game da batun raba tallafin rage radadin da dokar kullen ta haifar a fadin kasa.

Ya zuwa jiya Lahadi dai, Najeriya na da akalla mutane 5,959 da aka tabbatar sun kamu da cutar, wasu 1,594 kuma tuni aka sallame su bayan an tabbatar da wakewarsu, yayin da mutum 182 kuma suka riga mu gidan gaskiya.