✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jawabin Shugaba Buhari na sabuwar shekarar 2020

Shugaba Muhammadu Buhari ya fara da yi wa ’yan Najeriya godiya kan zabensa da suka sake yi a watan Fabrairun 2019. Sannan ya yaba wa…

Shugaba Muhammadu Buhari ya fara da yi wa ’yan Najeriya godiya kan zabensa da suka sake yi a watan Fabrairun 2019. Sannan ya yaba wa abokan hamayyarsa da suka yi takara tare kuma suka dauki kaddara.

Shugaban ya kara da cewa ba zai sake tsayawa takarar shugabancin kasar a 2023 ba amma kuma ya sha alwashin inganta harkar zaben kasar a nan gaba.

Daga nan kuma shugaba Buhari ya nanata aniyarsa ta yaki da ta’addanci, inda ya ce “samar da tsaro na daga cikin manyan alkawuran da na yi a gangamin neman zabena na 2015.”

Sai dai kamar yadda shafin yanar gizo na BBC Hausa ya bayyana, shugaba Buhari ya ce duk da an sami wasu ’yan matsaloli kasancewar dakarun Najeriyar sun yi yaki ne da ’yan ta’adda da masu garkuwa da ’yan kungiyar asiri da dai sauran masu laifi, Najeriya ce ta yi nasara daga karshe. Buhari ya kuma yi alkawarin inganta jami’an tsaro ta hanyar sama musu kayan aiki na zamani da bai wa sojojin horo.

Shugaba Buhari ya kuma sake jaddada alkawarin da ya yi na yaye wa ’yan Najeriya talauci “a lokacin jawabin cikar Najeriya shekara 59 da samun ’yancin kai na yi alkawarin tsamo miliyoyin matasan Najeriya daga talauci a tsawon shekaru 10 hakan ne ya sa nake kara jaddada wannan batu.”

Har wa yau, Buhari ya ce “ma’aikata za su samu albashin da zai ishe su sannan su kuma ’yan fansho za su samu kulawa ta musamman.”

Dangane kuma da kasafin kudi na 2020, shugaba Buhari ya ce kasafin zai taimaka wajen cika burinsa na gudanar da sauye-sauye a kasar, inda ya yi wa majalisar dokokin kasar karkashin Sanata Ahmed Lawal godiya kan amince wa da kasafin ba tare da bata lokaci ba.

Sai dai Buhari ya yi wa tsohuwar majalisar ta takwas shagube “ba tare da wani dalili ba sun ajiye kasafin kudin har fiye da watanni bakwai kawai domin siyasa.”

Muhimman ayyukan da Buhari ya ce zai mayar da hankali a kai su ne:

Tituna 47 da za a yi a tsakanin 2020/21 da suka hada da hanyoyin da suka dangana ga tashoshin ruwa.

Manyan gadoji musamman gadar Second Niger Bridge.

Kammala ayyukan rukunin gidaje 13 karkashin tsarin samar da gidaje na kasa.

Kaddamar da filayen jirgin Lagos da Kano da Maiduguri da Enugu a 2020.

Kaddamar da shirin aikin gona a karkara a kananan hukumomi 700 a tsawon shekaru uku.

Kaddamar da shirin gandun kiwon dabbobi a Gombe.

Horas da ma’aikata 50,000 domin taimaka wa malaman gona 7,000 da ake da su.

Kaddamar da titin jirgin kasa na Lagos zuwa Ibadan da Itakpe zuwa Warri a watanni ukun farkon 2020.

Fara aikin hanyar jirgin kasa da za ta tashi daga Ibadan zuwa Abuja da kuma Kano zuwa Kaduna a farkon watannin ukun 2020.

Kara sakar wa harkar wutar lantarki mara domin bai wa masu sanya hannun jari damar samo da sayar da wutar lantarki.

Fara aikin ginin tashar wutar lantarki ta Mambilla a watannin shidan farkon 2020.

Fara aikin jan bututun iskar gas AKK gas pipeline, da OB3 gas pipeline da kuma fadada bututun iskar gas din na Escrabos zuwa Lagos a watanni ukun farko na 2020.

Daga karshe shugaba Buhari ya sake nanata aniyarsa ta yaki da rashawa da cin hanci.