✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jennifer Lopez za ta sake aure

Shahararriyar mawakiyar Amurka, Jennifer Lopez ta yi baiko da shaharraren dan wasan Baseball Aled Rodriguez. A hotunansu da suka yada a shafin sadar da zaumunta…

Shahararriyar mawakiyar Amurka, Jennifer Lopez ta yi baiko da shaharraren dan wasan Baseball Aled Rodriguez.

A hotunansu da suka yada a shafin sadar da zaumunta na Instagram an ga yatsar Lopez da zoben baiko, inda shi kuma Rodriguez ke farin cikin amincewa da ita a matarsa.

Idan dai auren ya yiwu, wannan zai kasance auren Lopez na hudu, Rodriguez kuma na biyu a rayuwarsu. A auretayyar da suka gudanar a baya kowannensu na da ’ya’ya biyu.