✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jerangiyar Ma’anonin Kalmar ‘So’ Daga Mabambantan Mutane

Mahmud Tafida Kabo (08028932763): “Kalmar so ita ce ratayuwar zuciya ya zuwa wani abu da take ganin yana da muhimmanci a gare ta, tare da…

Mahmud Tafida Kabo (08028932763): “Kalmar so ita ce ratayuwar zuciya ya zuwa wani abu da take ganin yana da muhimmanci a gare ta, tare da shaukin kasancewa tare da shi kuma ta ji an ambace shi a yayin hira.”

Usaini Iliyasu Charanchi (08065224569): “FDk, so wata halitta ce wadda Allah Ya halitta a tsakanin jinsi biyu, mace da namiji. Ku sani, zuciya wani bangare ne mai matukar muhimmanci a jikin dan Adam. Haka kuma idan har jijiya da jini, tabbas kwakwalwa ba za ta gaza ba wajen tura sakonni cikin jiki. Wadannan sassa guda biyu, su ne ke haduwa su bayar da so. A hausance kuma ana cewa so tsuntsu ne, ya sauka daga wannan bishiya ya koma wata kuma na yarda da haka, domin ni na gani. Ma’ana, hakan ya faru da ni daga budurwata muka samu sabani yau tsawon shekara daya da watanni. Shi ya sa ma har yanzu ba ni da budurwa.”

A’isha Kaduna (08182726765): “Da farko dai, so wani abu ne da ke tausasa zukatan masoya. So maruru ne kuma so ba ruwansa da mulki ko kudi. So shi ke haskaka zukatan masoya kuma ba ruwansa da nasaba ko cancanta kuma shi ke wanzar da aure a tsakanin masoya.”

Bashir Muhammad Kano (08066014182): “Tirkashi! FDk, ai ni idan mace ta zama mai kunya da ladabi da karamci a gare ni, musamman ma idan muka yi ido hudu da ita; to ni fa a nan ta ci ni da yaki. Ma’ana, ai kawai na yi mata don kuwa ba kira babu abin da zai ci gawayi.”

Isma’il Alkyabba Funtuwa (07039495283): “A tunanina, abubuwan da mace za ta yi maka ka gane tana kaunarka bai wuce ta nuna maka so da kauna domin Allah, ba domin wani abin duniya da ka mallaka ba. Sai kuma tausayi da rikon amana.”

S. Kulele Zone 4, Abuja (08029148415): “A gaskiya ina matukar kaunar mace ’yar asali, mai addini, mai tsoron Allah, mai yin sallar nafila da karatu.”

Al’amin Webstar (08023289288): “Tabbas wannan maudu’i abin sha’awa ne. So halitta ne da Allah Ya cusa a jikin halittarSa. Nakan gane mace na sona ta hanyar kalaminta da kallonta da kuma karamta duk wanda mace take so.”

Maryam G. Tafida Sakkwato (08160516384): “Hoho! So, So, So, kaddara fada kan kowa!! So wani sinadarin rayuwa ne, wanda ke taimaka wa rayuwar bil Adama ta fannin rayuwarsa. So abinci ne da kowa sai ya ci shi. So makaranta ce da ba wanda ba zai shige ta ba. Wayyo, so! so jini ne a kokon zuciyar kowace halitta, mutum, aljani ko dabba za ka ga suna son junansu. Don haka so suturar zuciyar kowa ne, ba wanda ba zai saka ta a zuciyarsa ba. So ruwa ne dandana harshen kowa. Ni zan iya fahimtar mai so na ta hanyar nuna mini kulawa da tausayi da kuma jin kunyata da zai rika yi. Kyauta ma alamar so ce. Hmmm, ina matukar son so!”

Magaji Safaya Masukwari, kafur Jihar Katsina (07033180893): “Idan kuna magana da mace, ka ga tana kallon ka tana murmushi, to a nan za ka gane cewa tana son ka.”

Sunusi Hashim Zariya (08038321593): “So wani abu ne da dan Adam ke ji a cikin zuciyarsa a lokacin da ya ga wani abun ban sha’awa, wanda ransa ya biya a kai. Kana iya gane mace tana son ka ta hanyar kulawa. A turance, ana cewa: “Lobe is all about care!”

Amiru Isa Bakori (07068147933):  “Ni na fahimci kalmar so na nufin mika wuya kacokan da sakankancewa. Abin da za a yi mani in gane ana sona shi ne, in ga ana kula ni, an damu da ni, ana yi mani fara’a, ba a yi mani gardama, a taya ni murna ko bakin ciki kuma a rika ba ni shawarwarin da zan samu nasara a rayuwa,”
***