✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jibgin jibar jita-jitar jirga jama’a

Tsirin tsirfa Tsefe-tsefen tsifa Tsokanar tsororuwar tsattsafa Tsegumin tsugudidin tsufa Tsangwamar taradaddin tube tufa   Arme Ararume An yi kememe A kai ta kame-kame An…

Tsirin tsirfa

Tsefe-tsefen tsifa

Tsokanar tsororuwar tsattsafa

Tsegumin tsugudidin tsufa

Tsangwamar taradaddin tube tufa

 

Arme

Ararume

An yi kememe

A kai ta kame-kame

An dai yi yayime-yayime

 

Soki-burutsu

Aura yai tutsu

Karairayin tashin tsuntsu

Laftun labaran mutsu-mutsu

Kanzon kurege ya watsu

 

Uwargida tai balaguro

An daina jinta a kwararo

Sai aka ce amarsu za a karo

Hira ta karade kowane taro

Wane shu’umi ne ya tunzuro

 

Burinsu ai ta karo

Baba da Inna su zaburo

’Yan kwaraku an gangaro

Wai za a tamna goriyar goro

Na kishiyar da aka kakaro

 

Inna ta ce kun makaro

Na riga na juyo

Kowa sai ya kewayo

Ana ta ina ta zagayo

A kashe wutar da aka kyallaro

 

Jibgin jibar jirga jama’a

Batu ne kamar ba’a

Sai yai ta yaduwa cikin samma’a

Makaryata an gaza ce musu a’a

Wannan karon kiris sui sa’a

 

Tashen kwaramniyar kwatsam

Kwaran-kwacam

Da kayan kwancam

Kararam

kwankwam

 

Jijjigar jigata jiki

Juyin jaki

Awarwaron aringizon awaki

Turmutsutsun tunkuyin tumaki

Tururuwar tattaki

 

Amarsun ango

Doridasonon farin dango

Kankambar karambanin kango

Hange-hangen hayin hango

Gungun gudunmuwar gigiwar gwaggo

 

Balullubar bulalar Baba

Basajen bugun babba

Barambaramar babatun buba

Yarfen yayimar ayaba

Dumuiniyar dube-duben  duba

 

Aka yi ta zuba zance

Ce-ce-ku-ce

Ka-ce-na-ce

Wane ne ya ce

Zaman zauren zaurance

 

Kisisinar kishiya

Kai-kawon kulle kucciya

Karatun kumshiya

Kwamraniyar kunkuru da bushiya

Kaudin kaudar kumbiya-kumbiya

 

Fancalen fincikar falleliya

Ficikar fatalin tsiya

Fankamar fariya

Firgicin fagamniya

Fangimar farfadiya

 

Mamakon Mama

Ai ta samu dama

Babban bakin ce-ce-ku-ce

Ya jiwo abin da ta ce

Lumar uwarjiki ce makama

 

Watan Akwatun-Babba ya kasance dibge da mukun-mukun makonnin makarkashiyar mamayar Mama mai makekiyar makarantar mutunta mutane, inda aka yi mata tashin-tashinar tashen KWARAN-KWACAM DA KAYAN KWANCAM, HAKURI YAYA. An dai tsiwurwurta wannan ta’asa ce sanadiyyar tsawon lokacin da aka dauka ba a ji duriyarta ba a fadar Tsaunin Bila da kafafen yada kwakwazo na kasar Haurobiya suka yi.

Kai wadansu da suka zarta gayauna da irin shuke-shuken dashe-dashe, har ma bazawa suka rika yi cewa, an shirya bikin ajo da kade-kaden taka rawar banjo, wai za a kawo wa Mama kishiyar hajijiyar  Hajo, Uwa-uba ma wadansu masu tsokane-tsokanen tsangwamar tsugudidin tsegumi, har tururuwa suka yi a mafuskantar alkibla da ke fadar mulki ta Tsaunin Bila, don yi wa ango da amarya du’a’in zaman lumana, in ma an raba goriyar goro su dan samu su tauna. Domin ta haka ne za su tabbatar da cewa su ganau ne, ba jiyau ba.

Tuni dai da na ji wannan ruwaya marar inganci, cike da ganganci, sai kawai na dauke ta a matsayin shashanci, duk da cewa na ga takardar gayyata da aka baza a shafukan fuskantar-bokoko da tukin tuwon titi da watso-watson-zufa, wato dai kafatanin kaftun kofaton kafofin karambanin kambama yarfen yari-yarin yadon yadiya da suka haifar da JIBGIN JIBAR JITA-JITAR  JIRGA JAMA’A.

Daukacin wannan lamari da ya auku ga mai dakin Baban-burin-huriyya, babban darasi ne ga mahukunta cewa, ana bin kadin wainar da suke toyawa a farfajiyar fadar mulki. Kuma lallai a makekiyar makarantar Mama a rika yin darussan daidaita dumuiniyar dagar amarsun alkinta aikin agogon ango, don kada a yi mana: Auratayyar amaren arme kememe ai ta rarume-rarume, ana ta kame-kame da yayime-yayime.  Kodayake dai wani hanzari ba rarewa a runtuma a guje ba, ta yiwu BALULLUBAR BULALAR BABA ce ko BASAJEN BUGUN BABBA, wadda ta kacame, ta zamo baram-baramar babatun Buba, a salon yarfen yadon yadiyar yayimar ayabar dumuiniyar dube-duben duba.

’Yan makaranta a yi karatun ta-natsu, gudun kada a karke da tsuwwa tsu-tsu ko fuffukar falle fuka-fukin tsuntsu; idan kuwa aka ci kasa, ana iya karkewa da jan cikin tsayuwar tsutsa. Domin irin hakan na iya haifar da jijjigar jigata jikin juyin jaki a dabaibayin awarwaron aringizon awaki da turmutsutsun tunkuyin tumakin tururuwar tattakin take-taken tabarbarewa.

Batu na ingarman karfen karafan karfa-karfa da dai wannan jibgin jibar jita-jitar jirgata jama’a, ai gara a ce an yi gangankon gangamin gamayyar gyaran girar gararumar gara, ta yadda za a kakaba wa ’yan matan jaba da gafiya da samarin-kusu sasarin sihirin susucewa. Yin hakan ya zama dole, domin a ranar nazarin ingancin kwakwalwa ta duniya an baje jidalin jadawalin jimurdar juyewar kwanyar dimbin Haurobiyawa, musamman masu jikkata kurungunsu da haramben handame haramiyar hallaka halaliyarsu.

Wannan na nufin da batu aka ce an baza kan KIDAN KOKON DUHUND-UNDUMDURUNDUM ko TSAWWALAR TSURKUN TSUKUKUN TSUKEWAR TSAKA-MAI-WUYA ba lallai ne su yi wani tasiri ba, tunda ’yan gyare-gyare irin na gyare da kurege ake bukata kawai, ta yadda za  a yi ta kwasar gararumar gwagwabar gara.

Kai kamata ya yi ma a baza jita-jita bazo-bazo cewa, “Gwamnatin Baban-burin-huriyya za ta yi wa talakawan kasar nan BELIN-AUTA,” musamman ma ganin bayan da ta garkame gingimemen gambun kan iyaka, masu fama da talalar talauci ke kara jigata. Domin kowane irin alfanu wannan na-mijin yunkuri ke tattare da shi, musamman wajen hana safarar kayan mamaye kwakwalwa da miyagun makamai, marasa galihu dai ke ta kara jin jiki. Kai a dai ci gaba da gashi, suya kuwa sai Ranar Sallah, ta yadda idan an samu salala, an hana wasu arcewa da sulalla, to babu wanda zai ji a salansa. Kun ga ke nan akwai yiwuwar ko dai mu daina marmarin samfarerar samfurin kasar Tayar-Landan, ko kuma mu ci gaba JIMIRIN JINKIRIN JAN-KARIN JIRAN JIMBIRI!

Kai ni ma ga jibgin jita-jitar jijjiga jama’a nan zan cillo, wato: a akwatun magana mai jini na yi kasake, na jiwo, wai BABA ZAI KWACE LASISIN KIDAN KOKON DUHUNDUNDUM DURUNDUM: DAMIN MATSABBAN DA IRO MUGUN MADAMBACI YA KWATO ZA A JINKA WA TALAKAWAN HAUROBIYA A MATSAYIN BELIN-AUTA; sannan kadarorin Samarin-kusu da ’yan matan jaba da gafiya za a cefanar da su, a dan raba wa kowa da kowa a kasar nan.

Duk za a gudanar da wannan namijin kokari ne da zimmar kawo karshen HALIN-BURTU: A BADDA KAMA, A YI BARNA! Tirkashi!

Bisa la’akari da turka-turkar tufkar da aka tafka, sai mu ce Haurobiyawan da suka baza jibgin jibar jita-jitar jirga jama’a, ba su kyauta wa al’umma ba. Domin ko an kama uwargida da tu’annatin tunkude KISISINAR KISSAR KASSARA KISHIYA, ai masu hakki na iya bin kadin hakkinsu. To ina ruwan biri da gada. Haka nan a banzar bazara kun cika mu da surutu rututu kamar Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ratatata!