✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jibi mace ta farko za ta yi alkalanci a gasar Ligue 1 ta Faransa

Stephannie Trappart ta zama mace alkalin wasan kwallon kafa ta farko a Faransa.  Hukumar Kula da Alkalan Wasa ta Faransa ta fitar da wata sanarwa…

Stephannie Trappart ta zama mace alkalin wasan kwallon kafa ta farko a Faransa.  Hukumar Kula da Alkalan Wasa ta Faransa ta fitar da wata sanarwa a ranar Talatar da ta wuce, cewa Stephanie Trappart ce mace ta farko da za ta yi alkalancin wasa a gasar rukuni-rukuni na Ligue 1 da maza ke fafatawa a Faransa.

Kafin ita, ba a taba samun wata mace da ta yi alkalacin wasa a gasar Ligue 1 a Faransa ba.

Stephanie dai za ta yi alkalancin ne a wasan da zai gudana a tsakanin kulob din Amiens da na Starsbourg a jibi Lahadi idan Allah Ya kai mu.

Stephanie Trappart tana daga cikin alkalan wasan da za su yi alkalanci a gasar cin Kofin Kwallon Kafa na Mata na duniya da zai gudana a Faransa a tsakanin ranakun 7 ga Yuni zuwa 7 ga Yulin bana. Hakan ne ya sa Hukumar Kula da Alkalan Wasa ta Faransa ta zabe ta a matsayin mace ta farko da za ta yi alkalanci a gasar rukuni-rukuni na Faransa wato Ligue 1.

Yanzu alkalin ta bi sahun takwararta ’yar kasar  Jamus Bibiana Steinhaus da aka zaba mace ta farko ta yi alkalanci a gasar Bundesliga ta maza a Jamus a shekarar 2017.