Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

…Jibi Man United za ta hadu da Chelsea

A jibi Lahadi ce za a fafata a gasar Firimiya ta Ingila a tsakanin kungiyoyin Manchester United da Chelsea.

Wasan zai gudana ne a filin wasa na United, Old Trafford da misalin karfe 4:30 na yamma agogon Najeriya.

ADVERTISEMENT

Masana harkar kwallo suna ganin wannan shi ne wasan da ya fi zafi a wannan mako a gasar.

Tuni kocin United Ole Gunnar Solksjaer da na Chelsea Frank Lampard suka shirya tsaf don fuskantar wannan wasa don ganin sun samu nasara.

ADVERTISEMENT

Magoya bayan kungiyoyin biyu suna fata duk kungiyar da ta samu nasara tamkar za ta ba su goron Sallah ne a wasan na jibi.