Search
Subscribe
Jibi Najeriya za ta kece-raini da Brazil

Jibi Najeriya za ta kece-raini da Brazil

A jibi Lahadi idan Allah Ya kai mu kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles za ta kece-raini da takwararta ta Brazil a wasan sada zumunta.

Wasan zai gudana ne a kasar Singafore kamar yadda jadawalin wasan ya nuna.

Wannan shi ne karo na biyu da kasashen biyu za su hadu a wasan sada zumunta tun bayan wanda suka yi a 2003 kimanin shekara 16 da suka wuce inda Brazil ta lallasa Najeriya da ci 3-0 a Najeriya.

Tuni kasashen biyu suka bayyana zaratan ’yan kwallon da za su fafata a wasan. Daga bangaren Brazil akwai dan kwallon Paris Saint Germain (PSG) na Faransa Neymar da Dani Albes na Jubentus da ke Italiya da Ferminho na Liberpool da sauransu yayin da a bangaren Najeriya kuwa an gayyaci ’yan kwallon da aka saba gayyata amma ban da Ahmed Musa.

Masoya kwallon kafa a ciki da wajen Najeriya sun zuba ido su ga yadda wasan zai kaya.

 

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin