✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jidalin jaddawalin jalli-joga

  An karkare kada kuri’a Sai fafutikar samun sa’a An kawo karshen yi wa juna ba’a An ji batuna ta cikin samma’a Aikata miyagun laifuka…

 

An karkare kada kuri’a

Sai fafutikar samun sa’a

An kawo karshen yi wa juna ba’a

An ji batuna ta cikin samma’a

Aikata miyagun laifuka mun ce  a’a

Zugar zuganyewar zababaka

Ta  haifar da baraka

Da rudanin shirya taruka

’Yan maula na kwaraka

Ba sa son daina wararar tufka

*

Jidali

Jerin  jaddawali

Jalli-joga

Jajjagen jaga-jaga

Juyayin juyin juya-hali

*

Masu harkalla

Suna ta zilla

Da kulla gilla

Don su sa wasu kwalla

Har ai ta lalala

*

An fasko masu badala

Da ke tsalle-tsallen tsula

Da kulla-kulla

Ga yawan kutunguila

Wata ran sai an tsala musu bulala

*

Kowa ya daura damara

Al’umma na bukatar kira

Hankula duk su tattara

Mu lalubo hanyar warwara

Mar mu tsira daga asara

*

Mai-duka Yai mana sutura

Mui ta kai wa juna ziyara

Zumun zumunta a hallara

Mui wa juna kara

Kar a debi dukiyarmu ai kakara

*

Ina ’yan siyasa

Ban da kulla dasisa

Ban da sa-in-sa

A bari mu ci masa

Kafin ruwan damu ya tafasa

*

Mu kyautata dangantaka

Rani, damina da kaka

A shawo kan turka-turka

Mu daina shakka

Da talaka ake harka

*

Janjamin jan-ragama

Janye jaye-jayen jan-rigima

Tuni aikin gama

An ce ya gama

Sai  mu nemi makama

*

Gusun da birnin Shehu

Al’umma na ihu

Sun gaza dora tukunya a murhu

An hana dura hatsi a buhu

Balle daure goriyar huhu

*

A birnin Dikko

Manyan dawa na kwankwadar koko

’Yan fashi na nan a loko

Sun yi dako

Jama’a an yi cirko-cirko

*

Jihar Zaman-fara

Ana ta kara

Masu garkuwa ba sa jira

Su ne a bakin masu hira

Dole ta sa a kai hattara

*

Masu mulki

Kui tsayin daki

A dauki kulki

Ai aikin kirki

Miyagu a taka musu birki

*

A birnin Dabo

An ce ba a dabo

’Yan boko na ta kwambo

Da bobo

Kashe fatari ne kwabo-da-kwabo

*

A lalubo bakin zare

A daina kai wa juna hare-hare

Munanan maganganu da harare-harare

Kishin al’umma ba kwanare

Sai an hada karfi a tare

*

A yasar da bambance-bambance

A daina ka ce-na-ce

Ko zaman zaure ai ta zance

Managartan manufofi kar mu mance

A aiwatar da ayyukan kulla kawance

*

A hana kwasar gararuma

Mui aiki girma-girma

A farmaki masu dama-dama

Komai a yi da kima

Ko a ce da dama

*

Mui wa kawunanmu masalaha

Mu sai komai da arha

Kar a buge da neman ahaha

A ci a sha

A ji dadin raha

*

Kasa ta washe, domin zababbakar zabukan shekarar dubu karamin lauje da sili da manuniyar kasa ta gangaro karshe, duk da cewa ana ta yawan hasashe-hasashe, amma abin da dai kawai ya rage shi ne furta batutuwa daga harshe, cewa ashe-ashe wadansu sun yi nashe-nashe da JIDALIN JADDAWALIN JALLI-JOGA. Koma dai mene ne aka tsuwurwurta  a wajen zaben rukunin shugabannin al’umma a fadin Haurobiya, sai a tuna komai na da NAKASU, illa dai kawai ana son kwatanta abin da za a ce SAMBARKA, in ma son samu ne a samu NAGARGARU, amma ba fandararru masu fasa mana garu ba.

Baban-burin-huriyya da gama-garin gwamna gwarangwam lallai ku yi bitar batutuwan darussan makon nan, ta yadda za ku yi wa daukacin al’ummar kasar abin da ya dace wajen kawar wa kowa-da-kowa DUMUINIYAR DUGUNZUMAR DARKAKIN DAMUWA.

Babban batun da ke gaban Haurobiyawa dai, shi ne, bayan duk mun karkare sambatu da surutu rututu kan sakamakon alkaluman JIDALIN JADDAWALIN JALLI-JOGA, ai sai mu umarci zababbu su daina yawan babatu ko kulla kutu-kutu, su zo su dukufa ka’in da na’in wajen tunkarar dimbin matsalolin da suka yi wa al’umma kawanya a kowane bagire na rayuwa. A shawo kan GARKUWAR GAGARA KUWWA; GARARAMBAR GARA GARKEN GARAKA, uwa-uba zaman kashe fatari a tsakankanin masu fuka-fukin tashi, ta yadda za a rage musu radadin fushi kada su zo suna bushi ko rike harsashi da balati mai washi, har su sa wasu su kwashi kashi, karshe a karke da lallashi turka-turkar takun saka kuwa su ce babu fashi.  Zababbun wakilai ban da rafkanuwar rafke al’umma.

’Yan makaranta ban da SUKA-DA-BURTSATSEN MAGANGANU game da sakamakon zabi-sonka a fadin Haurobiya, domin idan aka ga mummunar ta’asa a ko’ina aka tafka ta, to da hannun gama-garin al’umma da suka yi GWANGWAJEWAR GWANJON GANYEN GAYE da DAMBARWAR DANTSATSAR DAMATSA. Bisa wadannan dalilai ni ina ganin ya kamata a yaba wa Hukumar Zabi-sonka ta kasa, domin ta yi rawar gani ko da kuwa wani zai ce ai TAKA NA-ZUMBUDE ce.

Hakika akwai miyagun da suka yi DANNIYA DA MURDIYYA, HANDAMA DA BABAKERE. A duk inda suka samu sa’a akwai hadin gwiwar masu JAGWALGWALON JAGALIYA da SARA-SUKA; a duk inda irin wannan mummunar manufa ta ci kasa ko hakarsu ba ta kai ga ruwa ba, tabbas akwai al’umma masu kishi da ke da zakuwar ganin an kyauta yanayin zamantakewar Haurobiyawa, don gudun kada a karke da ZAMAN-TATTAKEWA. Lallai mu yi hattara, hankulanmu su tattara.

Batu na ingarman karfen karafuna tarragon kwangirin layin dogo, ba tare da laulayin wulwulawar hannayen agogo ba, sai da al’umma ta bayar da kafa aka samu sakamako a doron JIDALIN JADDAWALIN JALLI-JOGA. Wannan ne dalilin da ya sanya a kowane lokaci aka gudanar da zabi-sonka sai ka ji wadansu sun rankaya  kotu don yin korafi, ko ma a yi ta tafka shari’a ta ki karkarewa. Haurobiyawa mu sauya, mu ga sauyi managarci, ta yadda kowa zai daina nukuburci don kasa ta fita daga kunci.