✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

JIDALIN KISHIYA: Labarin Farida (1)

Alhaji Baba dan kasuwa ne, wanda Allah Ya hore wa samu daidai gwargwado. Kasuwancinsa na rufa masa asiri sosai, musamman ma ya samu bunkasa, inda…

Alhaji Baba dan kasuwa ne, wanda Allah Ya hore wa samu daidai gwargwado. Kasuwancinsa na rufa masa asiri sosai, musamman ma ya samu bunkasa, inda yake fita waje domin saro haja. Yakan je kasashen China da Dubai, wasu lokutan kuma ya je kasar Saudiyya.

Yana zaune da matarsa guda daya, wacce suka wanki juna tun saurayi da budurwa. Yau sun kwashe tsawon shekara 15 da aure kuma Allah Ya albarkace su da ’ya’ya shida, uku maza, uku mata. Duk tsawon shekarun nan, babu wanda ya taba jin kansu. Koda sun samu sabani ko rashin jituwa, sukan warware abinsu ba tare da wani ya ji ko ya gani ba.

Suna gara soyayya a kowane lokaci, wanda haka ya sanya har mutane ke tsananin mamakinsu. Uwargida Farida ta kasance mace mai tunani da sanin ya kamata. Tana kyautata wa mijinta, makwabta ma sun shaidi haka. Tana da hakurin zama da mutane, domin babu yadda za ta zauna da wata ko wata mu’amala ta hada ta da mutum, ka ji ya ba da shaidar banza a kanta.

***

Wata rana Alhaji Baba yana tafiya cikin motarsa, a kan Titin Zoo a birnin Kano, sai ya ga ana daga masa hannu, alamar ya tsaya. Wata kyakkyawar budurwa ce ke tsayar da shi. Ga shi kuma ya yi kokarin tantance fuskarta, ko ya shaida ta, amma bai fahimci inda ya lakance ta ba. Ya dai samu wuri bakin hanyar ya tsaya.

Yarinya ce kyakkyawa, mai matsakaicin shekaru. Ta ci uban kwalliya, kanta lullube da wani gajeren hijabi, hannunta makale da wata kyakkyawar jaka.

“Assalamu alaikum!” Abin da ta gaya masa ke nan lokacin da ta dan rusuna daidai kofar direba. Kanshin turare ya doki hancinsa.

“Wa’alaikumus salam.” Ya amsa tare da kara shiga cikin tunanin inda ya santa. “Malama, lafiya dai kuwa? Na ga kin tsayar da ni.”

“Gaskiya taimako nake nema. Ina son ka rage mini hanya zuwa Asibitin Murtala, wata kawata ce ke jinya a can.”

Abin da ta fada masa ke nan, cikin wata murya mai cike da albishir tare da sakin wani murmushi.

“Assha! Allah Ya ba ta sauki.” Abin da ya fada ke nan, tare da ba ta izini ta shigo gaban motar domin ya rage mata hanya.

Bayan ta shiga motar, Alhaji Baba ya kama hanya. Tafiya yake cikin natsuwa, a yayin da wakar Hausa ta zamani ke fesowa daga ingantattun lasifikokin da ke manne jikin kofofin motar. Sun samu kansu cikin shiru, ga alama wakar nan tana tasiri gare su.

“Ina fata dai ban takura maka ba ko?” Inji ta, ta karya tafiyar kuramen da suke yi. “Na ga kamar kana da uzuri, amma na tsayar da kai.”

“Kada ki damu, na riga na gama hidimata ta yau, gida za ni. Wani abin kamar sara kan gaba, ta bakin asibitin zan bi in wuce. Kin ga ba batun takurawa ke nan.”

“Ai kuwa godiya nake.” Ta fada cikin murmushi.

Haka suka ci gaba da tafiya, har dai ya taka birki a bakin Asibitin Murtala. Ba su rabu ba sai da suka gabatar da kansu ga juna. Ta gaya masa cewa ta kammala digirinta na farko a Jami’ar Bayero, kuma har ta yi hidimar kasa a Kaduna ta kammala. Sun canja lambobin waya da juna, ta yi masa godiya, sannan suka yi sallama. Ta shiga asibiti, shi kuma ya kada motarsa ya nufi gida.

Alhaji Baba ya sukwani motarsa cike da albishir tare da tunanin wannan yarinya. “Saratu….Saratu!” Ya fara tunani, tare da furta sunanta a hankali. “Amma yarinyar nan ta iya kwalliya, ga shi ta iya zaben turare. Kanshin turaren nan nata ya dace da daddadan kanshin da nake bukata.” Ya ci gaba da tuki, bayan da danjar da ta tsayar da shi ta ba shi hannu.

Ya dauko wayarsa da ke aje a dashibod, ya danna maballin da ya fito masa da jerin sunaye. Ya danna harafin ‘S’ wanda haka ya sanya duk sunayen da suka fara da harafin suka bijiro. Ya sake danna maballi har sunan ‘Saratu Albishir’ ya fito. Ya yi haka ne domin ya sake tabbatar da cewa lallai sunan nata ya adanu a wayarsa. Ta gaya masa cewa sunanta Saratu Dangoggo, amma sai ya adana sunan nata da lakanin ‘Albishir.’ Kamar yadda ransa ya riya masa, haduwa da ita ya sanya masa wani babban albishir, domin kuwa cikin lokaci daya ya rika tunanin cewa akwai bukatar ya yi soyayya da ita. A ganinsa, zai samu farin ciki da nishadi idan ya kasance tare da ita. Wannan takaitacciyar tafiya da suka yi tare, wacce ba ta wuce minti 15 ba, gani yake kamar sun yi awa 15. Bai so tafiyar ta tsaya haka ba, sakamakon yadda ya samu kansa cikin shauki da annashuwa.

Haka dai ya ci gaba da tafiya, har ya isa kofar gidansa da ke Unguwar Danladi Nasidi. Bayan ya yi ham, dansa ya rugo ya bude kofa, ya murza motar cikin gida.

“Baba sannu da zuwa!” Inji Faisal.

“Sannunka dai. Har kun dawo makarantar kuma ina ’yan uwanka?”

“Suna cikin gida, mama ce ta ce in zo in bude maka, jin motarka ta tsaya bakin kofa.” Faisal ya ba shi amsa, tare da daukar jakar hannu daga bayan mota, ya shiga da ita gida.