✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

JIDALIN KISHIYA: Labarin Farida (12)

Tunda Alhaji Baba ya sanya kafa ya fita daga gida, misalin karfe biyu na rana, Uwargida Farida ba ta samu sukuni ba. Hankalinta ya yi…

Tunda Alhaji Baba ya sanya kafa ya fita daga gida, misalin karfe biyu na rana, Uwargida Farida ba ta samu sukuni ba. Hankalinta ya yi matukar tashi, musamman da ta fahimci cewa mijinta zai je wajen wani biki da aka gayyace shi. Ita dai a iya saninta da shi, ba mutum ba ne da ya saba halartar bukukuwa haka. Iyakacinsa daurin aure, shi ma sai wanda yake da matukar muhimmanci gare shi, kamar na amininsa ko kuma wani dan uwa da ya zama dole.

Tun bayan da ta ga kwafin katin gayyatar da aka aiko masa ta shiga damuwa, musamman ganin cewa wannan biki ba na aure ba ne, ba na haihuwa ba. Haka kuma ba bikin saukar karatu ko yaye dalibai ba ne. Biki ne na taya murna ga wata budurwa, kawai don zagayowar ranar haihuwarta.

“To, ita kuma wannan wace ce, wai ita Binta?” Farida ta takarkare da tunani. “Shin ita kuma mece ce dangantakarta da mijina da har za ta gayyace shi biki? Ni dai na san waccan sunanta Saratu. To ko dai ya fara neman mata ne barkatai haka?”

Duk tsawon yinin nan, tunanin da take yi ke nan. Koda ta samu gano katin gayyatar nan daga jikkar mijinta, ba ta bar al’amarin sasakai ba, sai da ta dauki mataki. Na farko dai ta yi kokari ta gano adireshin wurin da za a gudanar da bikin, sannan kuma ta yi kokarin gano sunan DJ din da zai yi wasa a yayin gudanar da bikin.

Ta hanyar waya da wata kawarta, wacce a unguwarsu DJ din yake, ta samu ganawa da shi ta waya. Ta ba shi kwangilar tattaro mata hotunan bidiyo na yadda bikin ya gudana. Naira dubu goma ta yi alkawarin biyansa ladar wannan aiki, shi kuwa ya yi alkawarin zai yi abin da ta bukata. Ya amince cewa da zarar an kammala bikin, zai tura mata bidiyon ta turakarta a WhatsApp.

Koda ta kammala Sallar Isha’i, Farida ba ta sake yin wani abu ba. Hasali ma a kan shimfidar ta yi zamanta, nan inda ta kammala Sallar. Ko abincin dare ba ta iya ci ba, babu abin da take sai kai-komo da tunani iri-iri. “Wai a yau ni ce na zama tamkar bora a gidan aurena. Duk irin wannan zama da muka yi da irin wannan soyayya da muka buga ko muke bugawa da Daddy, tsawon shekaru, wai shi ne yau yake neman yi mini kishiya?”

Ta buga wata doguwar ajiyar zuciya, sannan ta ci gaba da sake-saken zuci. “Shin wane mataki ya kamata in dauka kan wannan al’amari? Har ga Allah ba na son zama da kowace irin kishiya. To wai ma me na rasa na ’ya mace, mene ne ba na yi masa?”

Ta mike tsaye, ta nufi daki, ta nufi wajen dogon yaro, ta zauna kan doguwar kujerar da take kwalliya. Dakin a haskake yake, domin kuwa kwayayen lantarki sun maida shi tamkar da rana. Ta kalli fuskarta a madubi, ta lura da yadda dogon hancinta ya sauko kasa, ga dara-daran idanuwa masu dauke da doguwar gira. Nan take ta yakice hijabin da ke lullube da kanta, ta barbazo da kashin kanta, wanda ya kwanta a gadon bayanta. “Duk macen da ke da yalwar gashi irina, masana halittar mata sun ce mace ce ta musamman. Allah Ya ba ni diri da tsarin halitta, to me wannan mutumin yake so da har zai nemi hada ni da wata annoba, wai ita kishiya?”

Ta mike tsaye, ta juya baya, sannan ta dauki hannayenta ta rike kugunta da su. Ta waiwayo ta kalli yadda surarta take a madubi. “Ba batun koda kai ba, kuturina, kuturi ne girkakke kuma dirarre. Ba zan mance ba, kawata tun muna ’yan matanci take kirana da lakanin ‘Kwalbar Koka-Kola’ saboda damewar cikina da bajewar kuturina!”

A daidai wannan lokacin sai ta ji karar waya, alamar ana kiranta. Nan da nan ta yanke wannan tunani da take yi. Ta dauki wayar, ta samu cewa DJ ne ya bugo mata.

“Halo, DJ, kana lafiya?” Ta tambaya.

“Lafiya kalau Hajiya. Da ma ina sanar da ke ne, cewa taro ya tashi lafiya kuma na cika alkawari. Ki duba wayarki, na turo miki bidiyon yadda bikin ya gudana. Amma a gaskiya za ki sha mamaki.”

“Madalla! Na gode sosai, kada ka ji komai, insha Allahu da safe za ka amshi kudinka a hannun kawata, ’yar unguwarku da ta hada ni da kai.”

Ta duba agogon wayarta, ta samu karfe 10:30 na dare daidai. Nan da nan ta yi saurin bude turakarta ta WhatsApp, tana laluben bidiyon da DJ ya turo mata.

 

Taskar Filfilon Dausayin Kauna (FDK)

Yauwa! Yau ma FDK a shirye nake. A yayin da nake kurbar sassanyan zobo kuma na fara dauko sakonninku daya bayan daya ina karantawa.

Daga Mara Suna:

“Salam FDK, fatar alheri a gare ka, kai da sauran masu bibiyar wannan shafi mai albarka. A gaskiya muna jin dadin wannan labarin, Allah Ya kara basira amin.

Daga Abdulmalik Kabir Ghude:

Asslamu alikum FDK, jinjina da gaisuwa mai tarin yawa ga Uwargida Farida. Ina ba ta shawarar ta dage da addu’a saboda Saratu na son wargaza mata farin cikinta, sannan ta ja kunnen Alhaji Baba. Ya yi hankali da ’yan matan zamani. Daga karshe, a mika min gaisuwata ga Baban Sadik, na gode.

Daga Hameed Nura Fresh Boy (09067176209):

Allah Ya taimaki FDK tare da yi masa fatar kwana cikin koshin lafiya.

Daga Malama Zainab:

Barka da rana. Ni ma’abociyar karanta jaridar Aminiya ce kuma ina bibiyar shafinka na FDK, yana matukar nishadantar da ni. Godiya mai tarin yawa ga jagoran wannan shiri, Allah Ya raya zuriya, amin.

Daga Idris Muhammad Sabo Potiskum Jihar Yobe:

Assalamu alaikum, Malam Bashir sannu da kokari, da fatar Allah Ya kara tsawon rai tare da imani da natsuwa. Malam Sa’adu kuma Allah Ya gafarta masa bisa wannan wa’azi da ya gabatar shekara 66 da suka gabata. Da manyammu sun yi aiki da shi, astagafirullah da mun samu saukin rayuwa. Fatata Allah Ya sa mu fadaku da abin da Malam ya nusasshe mu cikin wannan wake nasa da ya gabatar, amin. (Malam Idris yana tsokaci ne dangane da sharhin da nake gabatarwa a shafin Gizago game da waken marigayi Malam Sa’adu Zungur na “Arewa: Jamhuriya Ko Mulukiya).

Daga Sulaiman Muhammad Masanawa Kabo:

Salam FDK, fatar alheri gare ka da masu bibiyar wannan shafi naka na Dausayin Kauna. Allah Ya kara zumunci, amin. Ina so ka isar min da sakon  gaisuwata ga masoyiyata A’isha Aminu da ke Hotoro Kano.

Daga Ikra Isah ’Yantakori Katsina (08036141059):

FDK, fatar alheri gare ka da duk ma’abuta bibiyar wannan dandali mai albarka. A gaskiya ni dai ina gidan Farida Uwargida. FDK, haƙiƙa ka cika jarumi kuma haziƙin marubuci, wanda salon rubutunsa ke da matuƙar burgewa, musamman ma Labarin Farida da Alhaji Baba. Allah Ya kare ka daga dukkanin sharrin masu sharri.

Daga Alhaji Salisu Aliyu:

Malam Bashir, ina yi maka fatar alheri, Allah kuma Ya kara maka basira, amin. Wallahi na karanta labarin da ka rubuta mai taken ‘Rayuwar Duniya: Labarin Malam  Shagalalle.’ Wallahi labarin ya fahimtar da mu sosai. Allah Ya kara maka basira da hazaka, amin summa amin. Ka huta lafiya.

Anisat Abdullahi Adamu Daura (07067716102):

Assalamu alaikum da fatar kana lafiya. FDK, ina gidan Saratu. Za su yi zaman lafiya tare da girmama juna a  tsakaninta da Farida. Don sai an gwada akan san na kwarai. Daga karshe ina son sanar da mata cewa, wani karin aure alheri ne, tamkar walkiya ce wadda halin kowa zai bayyana.

Daga Rabi’u Ibrahim CKKW (08135421198):

FDK, wannan labari na Farida yana nishadantar da ni dari bisa dari. Bayan haka ina fatar alheri ga ’yan uwa ma’abuta bibiyar wannan shafi. Allah Ya bar zumunci, amin.

Daga Dan Jos (Najodan):

Shawara: FDK, a karshen labarin, ka rubuta sunayen masu kuri’a ko lambobinsu. Ni dai ina bayan gaskiya, ina gidan Saratu. Labarin dai akwai nishadi.