✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

JIDALIN KISHIYA: Labarin Farida (13)

Lokacin da Alhaji Baba ya kai Saratu gida, ba ta bar shi ya tafi nasa gidan ba, sai da suka kwashe lokaci mai tsawo suna…

Lokacin da Alhaji Baba ya kai Saratu gida, ba ta bar shi ya tafi nasa gidan ba, sai da suka kwashe lokaci mai tsawo suna tadi. Bai ankara ba, ya duba agogo sai ya ga har karfe sha daya da rabi. Nan take hankalinsa ya tashi, ya yi ban-kwana da ita, ya tada motarsa ya nufi gida.

Ya kamo hanya cikin sauri, kokarinsa ya isa gida. Hankalinsa kacokan ya koma gida, ya fara tunanin irin abin da zai tarar daga wajen matarsa. Nan take ya yi ta kai-komo da tunani iri-iri, musamman ganin yadda ya raba dare a waje.

“Na mance lokacin da na kai karfe goma sha dayan dare a waje!”

Bai san lokacin da ya furta wannan kalami ba, domin kuwa ya samu kansa cikin kaduwa.

Yana cikin tafiya, sai kawai ya ji bayan motarsa ya yi kasa. Nan take ya koma gefen hanya, ya sauko daga motar domin duba abin da ya faru. Bayan ya sauko ne sai ya iske ashe tayar motarsa ce ta baya ta yi faci, iskar duk ta fice. Hankalinsa ya kara tashi. Ya duba agogo ya ga sha biyu saura kadan.

“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!”

Abin da ya fada ke nan, kafin daga bisani ya dauko safaya-taya da jak domin sauyawa.

Da kyar ya samu ya daga motar, inda yana kan aiki sai wayarsa ta kunna. Ya duba sai ya ga Saratu ce take kira. Ya dauka sai ta tambaye shi ko ya je gida? Shi kuma domin kada ya cakuda al’amarin sai ya ce mata ya dai kusa.

“Na kusa isa insha Allah. Idan na isa zan sanar da ke.”

Abin da ya fada mata ke nan, inda ya kashe wayar.

Yana kashe wayar, sai ga wani kiran ya shigo. Wannan karon kuma Uwargida Farida ce take kira. Nan fa ya yi kasake, yana son ya dauki kiran kuma wata zuciya tana hana shi. Daga bisani dai ya cije, ya dauka.

“Hala wajen shagalin za ka kwana ko?”

Abin da Farida ta fada ke nan cikin wata kakkausar murya.

“Ya Salam!” Abin da ya fada ke nan. “Shin da wanne zan ji? Don Allah ki sama mini lafiya, ga ni nan na samu matsala da tayar motata.”

“Matsala kuma? To Allah Ya yi mana maganin matsala. Matsala kuwa na tattare da mai nemanta, domin kuwa mutumin da ka haura shekara arba’in amma kana zuwa shagalin bikin mata, ai kuwa ka gamu da matsala. Yanzu ne ma matsalarka ta fara. Idan ka ga dama ka kwana can…”

Bai bari ta ida magana ba sai ya kashe wayar, ya maida hankali wajen daura tayar.

 

***

Karfe daya saura kwata daidai ya kwankwasa gida amma babu wanda ya bude masa. Ya ci gaba da buga korfar gidan, sai da ya buga fiye da sau shurin masaki amma babu wanda ya bude masa. Ya buga wani uban tsaki, ya koma cikin mota ya zauna, ya yi kasake!

Bayan kamar minti ashirin yana zaune cikin mota, sai ya dauki waya ya buga wa Farida. Wayar ta dauki lokaci tana kara, amma ba ta dauka ba. Ya sake bugawa, nan ma shiru. Sai da ya buga wayarta fiye da sau goma amma ba ta dauka ba. Nan ma ya buga tsaki, zuciyarsa ta yi mugun baci.

Bayan kamar minti biyar, sai ya koma bakin kyaure ya yi ta bugawa. Sai can daga bisani aka zo aka bude. Ba Farida ce ta bude ba, daya daga cikin ’ya’yansa ce ta bude.

Da ya shiga gida, ya iske Farida zaune a kujera ta yi kasake. Ya zauna kusa da ita, har ya daga kai zai yi mata magana, sai ta riga shi.

“Har ka gama rabon furen?”

Abin da ta fada ke nan cikin gatse.

“Fure? Wane irin fure kuma?”

Fuskarsa a hargitse cikin mamaki da gigita ya yi mata wannan tambaya.

“Ka ji ni da kyau amma bari in kara maimaita maka; shin har ka gama raba furen? Ba kai ne jure fari sai tofa ba, kai ne nata fure?” Ta sake yaba masa bakar magana, tare da yanko wani baiti daya na ‘Wakar Fure’ da aka kada musu a wajen biki.

Nan fa suka ci gaba da maida wa juna magana. Ya ce kaza, ita kuma ta ce kaza. Duk tsawon daren nan, babu wanda ya runtsa a cikinsu.