✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

JIDALIN KISHIYA: Labarin Farida (14)

A ci gaba da wannan labari, mun tsaya ne daidai inda Alhaji Baba ya dawo gida da tsakar dare daga wurin bikin ranar haihuwar kawar…

A ci gaba da wannan labari, mun tsaya ne daidai inda Alhaji Baba ya dawo gida da tsakar dare daga wurin bikin ranar haihuwar kawar budurwarsa. Ya iske matarsa Farida cikin fushi, inda nan take ta fara kalubalantarsa, musamman dangane da bidiyon bikin – abin da ya haddasa suka ci gaba da canjin miyau. Yanzu kuma za mu ci gaba:

 

Wani gululun bakin ciki ya tokare makoshin Alhaji Baba, a lokacin da matarsa ta zayyana masa dalla-dalla yadda bikin nan ya gudana. Ba wannan ba ma, hatta wakar ‘Fure’ da aka sadaukar a gare shi da budurwarsa a wurin bikin sai da Farida ta rera masa.

“To yanzu ke da kike wannan karar da kanzon kuregen, duk wa ya sanar da ke cewa abin da ya gudana ke nan a wurin da na je?” Abin da ya gaya mata ke nan, yana ta huci kamar wani bakin maciji da ke shirin kai sara.

Farida ta saki wani murmushi wanda ya fi kama da yake, ta ce: “Allah Sarki! Wato har ma shaida kake nema ko, bayan kai da kanka ka san abin da nake fada gaskiya ne? To, ba ni aron ’yan minti biyu ka kalli wannan bidiyo?”

Ta kunna bidiyon da ke jikin wayarta, ta mika masa. Nan da nan ya amsa ya kura ido dara-dara kamar na autan kururu, yana kallo. Irin yadda ya tattara hankalinsa a kan bidiyon nan, kai ka ce an tada kabbarar Sallah ne, yana gaban sahu.

Farida ta kalli yadda mijinta ke ta faman kallo, jibi na keto masa kamar wanda ya hadiyi karin kunama. Bayan ya kammala kallon bidiyon, jikinsa ya yi sanyi. Ya mika mata waya, ya koma lakwas kan kujera, idanuwansa wuri-wuri, ya kasa hada ido da matarsa.

“To, me kuma za ka ce? Ko kuwa kana son wata shaidar daban?”

“Kin ga, don Allah mu bar maganar nan. Ni dai har ga Allah ba ni da wani mugun nufi ko wata bakar aniya gare ki ko iyalina. Ki sama mini lafiya da batun nan, don Allah.” Abin da ya fada ke nan babu ko sassautawa, kalma na dukan kalma, kamar mai in’ina.

“Iyeee!” Ta tabe baki. “Karfin hali ke nan, inji masu iya magana, wai barawo da sallama.” Yanzu ka kalli wannan rundunba da kake aikatawa a garin nan amma ka ce in sama maka lafiya? Yanzu da girmanka da mutuncinka a gari, ga ’ya’yanmu suna kawo karfi amma kana yin halayen da ko samarin zamani sai haka, kuma ka ce kada in yi magana?”

“Me kike nufi?” Da murya mai karfin sauti ya fara magana. “Me na aikata na Allah wadai? Kin kama ni ina fasikanci ne ko kuwa an gaya miki ga ’yan sanda sun kama ni da laifin sata ne? Shin, kin bankado sirrin cewa ni maye ne na kama kurwar wani ko wata ce? Haba..haba.. ya isa haka nan, don Allah!”

Ta kyalkyace da dariya, ganin yadda mijinta ya dauki wata siffa da ba ta taba ganinsa cikinta ba. Duk tsawon zamansu na aure, ba ta taba ganin ya harzuka haka ba. Ta yi mamakin yadda yake ta sakin huci, kamar zai kai mata duka, kamar an ce masa ta kashe masa da.

“Wato na zama abin dariya ma ke nan ko? To, bari in gaya miki da babbar murya. Maganar aure gaskiya ce, aure zan yi kuma wannan yarinya da kika gani a bidiyo, ita zan aura.”

Farida ta yi shiru, ta kura masa ido kawai.

“To wai ma ni in tambaye ki, shin wane munafuki ko wace munafuka ta kawo miki wannan bidiyon? Ko kuwa fita kika yi daga gidan aurenki, kika zo wajen bikin, kika dauka da kanki?”

Ba ta ce masa uffan ba, ta dai kura masa ido. Bayan wani lokaci, sai ga ’ya’yansu duk sun tashi daga barci, sun fito daga dakunansu. Cece-ku-ce da hayaniyar iyayensu ce ta tayar da su. Yaran ba su ce komai ba, sun saka hajar mujiya ga iyayensu.

“Wa ya ba ki izinin fita zuwa wajen bikin nan?” Ya yunkura zai amshi wayar daga hannunta, ita kuwa ta kunshe abarta cikin hannu. Ya so ya kama ta da kokuwa amma daya daga cikin ’ya’yansa ta zo ta kama hannunsa, tana ba shi hakuri. Nan take ya dawo cikin hayyacinsa.

Farida ta rasa abin da za ta yi, ta fashe da kuka. A cikin kukan ne take magana. “Wannan takaici da me ya yi kama?”

A cikin daren nan ta bude kofa ta fita waje, daga ita sai suturar jikinta. ’Ya’yanta suka bi bayanta suna cewa ta dawo gida amma ba ta saurare su ba. Sai da gari ya waye ne Baba ya samu tabbacin cewa yaji ta yi. Ba gidansu ta tafi ba, gidan yayarsa Tabarno ta kwana.