✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

JIDALIN KISHIYA: Labarin Farida (2)

*Assalamu alaikum!” Alhaji Bako ya shiga falon gidan, inda ya iske matarsa da wadansu daga ’ya’yansa suna kallon wani fim din Hausa. “Wa’alaikumus salam, warahmatullah!…

*Assalamu alaikum!” Alhaji Bako ya shiga falon gidan, inda ya iske matarsa da wadansu daga ’ya’yansa suna kallon wani fim din Hausa.

“Wa’alaikumus salam, warahmatullah! Daddy, sannu da zuwa.” Matarsa Farida ce ta amsa masa sallama, tare da mikewa tsaye daga kan kujerar da take zaune. Sauran yaran ma suka tashi tsaye, sannan suka gaishe shi.

Yana shirin zama ke nan sai wayarsa ta fara karaurawa. Ya duba sai ya ga sunan Saratu Albishir ya fito. Ganin haka sai ya yi wa turakarsa tsinke. Dama kofar turakar tasa na daga gefen dama, daga cikin falon.

“Ta Musamman, bari in shiga daga ciki, zan yi wata waya mai muhimmanci.” Abin da ya fada ke nan, a yayin da ya sanya hannu ya latse wayar.

“Haba Daddy, har gida ma ba za su bar ka ka huta ba? Ai ya kamata su kyale ka ka sarara, kasuwanci a waje kuma kasuwanci a gida? Amma babu damuwa Daddy,” inji Uwargida Farida. Da ma kallo muke, kafin su dauke wutar nan.”

Irin yadda suke samun fahimtar juna tunda suka yi aure, shekara 15 da suka gabata ya sanya suke zaune tamkar abokai. Babu mai jin kansu -abin da ya haifar da farin ciki a tsakanin ’ya’yansu. Dalilin fahimtar ce ma ta sanya ita ba ta kiran sunansa kai-tsaye, sai dai ta ce Daddy. Shi kuwa a nasa bangaren, ba ya kiran sunanta tsirara, sai dai ka ji ya ce mata ‘Ta Musamman.’ Idan ma suna cikin annashuwa, musamman idan sun kadaice, za ka ji yana yi mata lakani da ‘FATA’ (Farida Ta Musamman).

Wayarsa ta kara kadawa, a daidai lokacin da ya shiga turakarsa. Ya dauki wayar, bayan ya danna maballin amsa kiran. “Assalamu alaikum… halo, halo.” Abin da ya fara fada ke nan, lokacin da ya murza hannun kyauren dakin da nufin rufewa. Ya samu kujerar kushin da ke cikin turakar ya zauna, tare da natsuwar amsa wayar.

“Malama Saratu.” Ya fada cikin wata murya mai cike da natsuwa tare da shauki. “Yaya jikin kawar taki? Ina fata da sauki.”

“Alhamdu lillahi!” Inji Saratu. “Ta samu sauki, ina zaton ma kila gobe a sallame ta. Yaya ka isa gida lafiya?”

“To, Allah Ya kara sauki. Kin ga na yi ragon azanci, ya kamata a ce na shiga asibitin na duba ta dazu da na ajiye ki a bakin kofa.” Ya fadi haka, tare da sakin wani murmushi, kai ka ce yana kallon Saratu gaba-da-gaba, ba wai a waya suke magana ba.

“Haba dai…” Ta fara wata siririyar dariya. “Ai babu komai, addu’ar ma da ka yi ta isa.”

“Haloo.. halo.. Alhaji kana ji na? Lafiya dai kuwa?” Saratu ta ji layin ya yi shiru, jim kadan da ta ji wata kururuwar yarinya daga bangaren Alhaji Baba.

A daidai lokacin da suke tattaunawa ce, sai Alhaji Baba ya ji kururuwar ’yarsa a falo, alamar wani abu mai hadari ya faru da ita. Nan take ya katse waya, ya mike zambur tare da bazama da sauri wajen kofa. A lokacin da ya bude kofar, ya shigo cikin falon da sauri, kafin ya isa inda yake nufin kai ceto, sai ya ci karo da karamin teburin da ke tsakiyar falon. Ya fadi warwas a shimfidar falon, wayarsa ta kubuce daga hannunsa, ta gara zuwa daidai kafar matarsa, Farida.

“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!” Farida ta fadi haka, lokacin da take tallabe da ’yarta. “Sannu! Da fatan ba ka ji rauni ba.” Fuskarta cike da damuwa, yayin da sauran ’ya’yansa da ke falon suka yi tsaye cirko-cirko.

“Lafiya…lafiya?” Inji Baba, bayan ya mike tsaye, ya nufi wajen da matarsa ke rungume da yarinyar da ta fasa kara. “Me ya same ta?” Ya kai hannunsa yana shafa fuskar ’yar tasa, wacce ita ce mafi karancin shekaru cikin ’ya’yansa.

“Ta samu tsartuwa daga wayar wuta.” Inji Farida, a yayin da take kokarin jijjiga yarinyar. “Ni kaina ban ankara da lokacin da ta kama wayar wutar ba. Ka san na gaya maka shekaranjiya, cewa a gyara wayar jikin soket din can, domin ta fito fili.”

“Sannu Mama.” Ya tausaya wa yarinyar, wacce lakanin da suke kiranta da shi ke nan, kasancewar sunan mahaifiyar Farida gare ta. Baba ya amshi yarinyar daga hannun Farida, ya ci gaba da duba ta. “Ko dai mu tafi asibiti ne, a duba ta sosai?” Ya tambaya, a lokacin da ya kura wa ’yar tasa ido cike da tausayi.

A daidai lokacin ne kuma sai wayarsa, wacce ke yashe kusa da kafar Farida ta buga, alamar ana kira. Nan take hankalinsa ya tuno masa da batun tattaunawar da yake da Saratu. Hankalinsa ya tashi, domin kuwa ya kyautata zaton cewa ita ce ta sake bugowa, musamman ganin cewa ba su gama magana ba ya katse maganar, sanadiyyar wannan abu da ya faru da ’yarsa. Ga shi kuma wayar ba a hannunsa take ba, don haka ba zai so matarsa ta gane cewa mace ce ta bugo masa waya a wannan lokaci ba.

A lokacin da Farida ta kai hannu za ta dauki waya, shi ma Alhaji Baba ya yunkuro zai dauka, a lokacin da hannunsa daya ke tallabe da yarinyar a kirjinsa. Hannun matarsa ya riga nasa damkar wayar, idanunta kuwa sun kai ga fuskar wayar. ‘Saratu Albishir.’ Sunan da ta ga ya bayyana ke nan a fuskar wayar, wanda ya sanya ta wangale baki da alamar mamaki.

Alhaji Baba ya lura da yadda fuskar matarsa ta canJa, kamar wadda kunama ta harba. Ya bude baki zai yi magana, amma ya nemi kalmomin da zai furta ya rasa. Kafin ma ta miko masa wayar, har adadin sautin kiran ya mutu. Don haka ya fasa cewa komai, ya mika hannu ya amshi wayarsa.

***

Sakonnin Fatan Alheri

FDK na fatan alheri ga mai lamba 08967653314, wanda bai aiko da sunansa ko adireshi ba.

*Daga Teema (FUT), wacce ta yi tsokaci game da Labarin Farida, tana cewa: “Hmm. Lalai kam akwai babban jidali! Ita kadai ta san dalilinta na tsaida Alhaji Baba, Allah Ya sa mu dace amma don Allah kada a bayyana lambata.”

*FDK na yin fatan alheri ga Ahmed Kudi Masussuka, 08081266888.

*Shi kuwa Dahiru Sunusi Gwangwan Rogo LGA, Jihar Kano, mazaunin birnin Abuja, ya aiko cewa: “Assalamu Alaikum, ina so ne a gaida mIni da rabin raina, Sahaibe Usman.

*Nasiru Kainuwa Hadeja, 08100229688 yana cewa: Rayuwar matashi ba sauki – yawon dare (zuwa hira) kiran ’yan mata a salula, wankan yamma. Wanki da guga babu kakkautawa, mu’amala da masu turare (yau a sayi wannan gobe wancan kalar) duk don a burge ’yan mata. Haka su ma ’yan mata a nasu bangaren ba sauki, safe, rana, dare wata sai ta shafa hoda. Wata tun kafin karin kumullo take shafa hoda a fuska, ta wanke kafarta ta shafe ta da mai. Hakazalika duk sanda za ta fita waje, ko ba ta yi wanka ba ta yi dakale, ta shafa hoda. Mai kaushin kafa kullum tana cikin goge kafar duk don mu (samari). Abin tambaya a nan shi ne, tsakanin samari da ’yan mata, wadanne suka fi wahaltuwa bisa la’akari da irin dabi’un da na zano?”