Search
Subscribe
JIDALIN KISHIYA: Labarin Farida (3)

JIDALIN KISHIYA: Labarin Farida (3)

Wannan wani gajeren labari ne mai dauke da darussa masu yawa, na samu tabbacin cewa labarin ya faru da gaske, don haka ni FDK, ganin muhimmancinsa ya sanya na fassara shi zuwa Hausa daga Ingilishi, na yi masa kwaskwarima tare da kare-kare, domin amfanin ’yan dandalin nan. Ga kashi na hudu nan a yau:

 

“Halo…halooo!” Saratu ce ke ta markabun magana a wayarta, duk da cewa ba ta ji amon layin da take kira ba. “Ko dai ya kashe wayarsa ce? To, me ke faruwa ne?” Tana ta jefa wa kanta tambayoyi, wadanda ita kanta ba ta san amsarsu ba. Tana cikin damuwa sosai, musamman ganin yadda ba ta dade da fara magana da Alhaji Baba ba, amma ya katse maganarsu. Ga shi kuma kusan fiye da sau goma ke nan tana bugawa amma yana latsewa, daga karshe ma ga shi da alamar ya kashe wayar tasa gaba daya. Ta buga uban tagumi cikin damuwa.

“SS, yau kuma ina ce lafiya dai ko?” Kawarta ce, Binta Mamman ta shigo gidan su Saratu, inda ta same ta ta yi tagumi, alamar da ke nuna cewa tana cikin damuwa.

“Ke dai bari Binta, yau SS ta koma SJ,” inji Saratu, bayan ta dago kanta zuwa gare ta. Kawayen juna ne, domin kuwa tare suka yi karatu a Jami’ar Bayero, don haka sun zama aminai. Binta ba ta cika kiran sunan kawarta kai-tsaye ba, sai dai takan kira ta da lakanin ‘SS’ wanda ke nufin ‘Senior Saratu.’

“Yau ban gane ‘SS’ ta koma ‘SJ’ ba, me ke faruwa ne?” Inji Binta, ta yi tsaye gabanta, hannuwanta rike da kugu, cikin mamaki.

“Yau na koma ‘Saratu Junior’ domin kuwa mutumin nan da nake ba ki labari, ya fara gwagwata ni. Kin ga na kira shi mun fara magana, amma na rasa kansa, daga karshe ma ga shi ya kashe wayar. Ban san dalili ba amma koma me ke nan, ina jin ba mai dadi ba ne.”

“A ina ne ya ce yake a lokacin da kuke wayar?” Binta ta tambaya.

“Bai sanar da ni ba, amma babu shakka a gida yake, domin akwai lokacin da na ji kamar hayaniyar yara.” Ta amsa mata, har yanzu fuskarta cike da alamar damuwa.

“Ayyaaa! Ga dalili nan kuru-kuru ya bayyana. Babu mamaki matarsa ce sanadi, kin san fa kishin tsiya na nan ga macen da ta dade ita kadai ba tare da kishiya ba a gidan mijinta.”

“Ummmm, ke ma fa kin zo da magana, babu shakka abin da ka iya faruwa ke nan,” inji Saratu. “Kin ga ni kuma duk ban kawo wannan a raina ba, na yi tsammanin ko wulakanci ne zai fara shiga tsakaninmu da shi tun yanzu, tun tafiyar ba ta je ko’ina ba.”

“Ko daya, musamman idan labarin da kika gaya mini gaskiya ne.” Binta ta dauki kujera ta aje kusa da kawarta, ta zauna. “Ke fa kika gaya mini yadda ya kidime a lokacin da ya rage miki hanya zuwa Asibitin Murtala. Ko kin mance yadda kika ce kin yi ta gara shi kafin ma ki amince ki ba shi lambar wayarki? Kin mance kin gaya mini cewa shi ya fara bugo miki, bayan ya isa gida? Wannan duk yana nuna yadda ya yi tsananin kamuwa da sonki ne.”

“To, yanzu dai kin ga yadda wankin hula ke neman kai ni dare. Tun yanzu kin ga yadda jirgin ke neman wuntsilar da ni a teku. Ina mafita?”

“Lallai kam abin na yi ne.” Binta ta fada, a lokaci guda kuma tana sosa keyarta domin karfafa tunanin irin shawarar da za ta ba kawarta.

“Kin san fa masu salon magana suna cewa, da sanyin safiya ake kama fara. Saboda haka duk matakin da ya kamata mu dauka, mu dauka kawai da wuri.”

“Tabbas, bori ba ya son sanyin jiki, zan yi duk abin da zan yi domin mallakar Alhaji Baba. Ba zan kara yin sakaci ya kubuce mini ba, kamar yadda ya faru da Dandauda.”

Ta ja wani gwauron numfashi, sannan ta samu kanta cikin shiru na dan takaitaccen lokaci. Wannan ya ba ta dama ta tuno da irin markabun soyayyar da suka yi da Malam Dandauda, wanda daya ne daga cikin malamanta a Jami’ar Bayero. Ta so a ce ya zama mijinta, kasancewarsa wanda bai yi auren fari ba, duk da cewa ya ba shekara talatin baya. Ta yi iyaka kokarin su yi aure, amma ya kekasa kasa ya kiya. Daga karshe dai ta gano cewa manufarsa da ita ba ta aure ba ce, dalilin da ya sanya ta cire wannan tunanin daga ranta, duk da cewa har yanzu suna “zumunci” da juna.

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin