✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jigawa ba ta da matsalar karancin abinci mai gina jiki – Ahmed Dansitta

Manajan Hukumar Bunkasa Aikin Gona na Jihar Jigawa (JARDA), Alhaji Ahmed Adamu Dansitta Gumel, ce batun cewa ana yunwa a Jihar Jigawa ba gaskiya ba…

Manajan Hukumar Bunkasa Aikin Gona na Jihar Jigawa (JARDA), Alhaji Ahmed Adamu Dansitta Gumel, ce batun cewa ana yunwa a Jihar Jigawa ba gaskiya ba ce. “Saboda haka na kalubalanci dukkan masu cewa akwai karancin abinci mai gina jiki a Jihar Jigawa domin jiharmu ta manoma ce kuma muna da abinci,” inji shi.

Manajan ya ce wasu  kungiyoyi ne suke bata sunan Jihar Jigawa suna cewa tana fama da matsalar karancin abinci mai gina jiki, inda ya bukaci su sauya tunani

Ya ce Gwamnatin Jihar Jigawa ta yi kokari wajen bunkasa harkar noman shinkafa, inda ya ce yanzu noman ya sa matasa da dama sun dogara da kansu saboda yadda gwamnati mai ci take taimaka wa matasan da kayan aikin noma a kan farashi mafi sauki.

Ya ce sun gano a noman shinkafa na bana, manoman shinkafa a Jihar Jigawa za su samar da tan dubu 15. Ya kuma nuna gudunmawar da Gwamnatin Jihar ta bayar wajen  tallafa wa manoman shinkafa musamman yadda gwamnatin ta samar da injinan casar shinkafa kanana a kan farashi mai sauki.

Ya kara da cewar yanzu haka gwamnatin jihar, ta raba wa manoma injin feshin kwari 4,500 da nufin kashe kwari masu lalata amfanin gona.

Da ya juya kan kiwo, cewa ya yi shirye-shirye sun yi nisa domin koya wa mutanen jihar dabarun kiwon awaki, wanda zai tallafa wa mata da kuma bunkasa tattalin arzikin mutane.