✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jihar Bawan-cici: Malam Ya-isa-Ya-yi-guda

Direbobin allin Jihar Bawan-cici da ke kasar Haurobiya sun ga tasku, inda Malam Ya-yi-guda ya kori jami’an koyar da watsattsake da buda wgagen littattafai har…

Mai ShelaDirebobin allin Jihar Bawan-cici da ke kasar Haurobiya sun ga tasku, inda Malam Ya-yi-guda ya kori jami’an koyar da watsattsake da buda wgagen littattafai har dubu kofar hanci. Haurobiyawa ka da a dauka cewa Gwamnan Jihar Bawan-cici ya tafka ta’asa, a’a, ba haka al’amarin yake ba. Domin shi a kyakkyawan gurgun karatun wasikar jakin dawansa, al’ummar Jiharsa ba sa bukatar direbobin alli. To wai ma duk dai bukatar ai a dumdume kwanyar ’yan dugwi-dugwi da Fura-mai-kyau, idan suka tasa kuma a sake su-su-dire. Gwamna da iyalansa sun sha sun koshi. Don haka ai ba sai kowa ya kwankwada ba.
A tsarin waskiya irin na Gwamnan Jihar Bawan-cici, yana ganin duk tsallaken badaken da direbobin alli suke yi, wani nau’i ne na tabin kwanya, kuma don me ma za su nemi karin ladar kweadago, alhali tun yana kwankwadar Fura-mai-kyau ya sha jin ana furta cewa ladar direbobin alli sai ranar gobe, don haka ma Manyan gobe ba sa sanya su a lissafi. Uwa-uba ’ya’ya da jikokin Gwamnan Bawan-cici ai ba a irin wadannan farfajiyoyin koyon watsattsake da buda wagagen littattafai suke kwankwadar fura-mai-kyau, ballantana su kai matakai a sake-su-su-dire. ’Ya’yan gama-garin al’umma ne ke gararamba a cikin ajujuwa, to “tunda babu dana ko jika, me zai sanya in rika kyautata wa direbobin alli?” A tunanin Gwamnan Jihar Bawan-cici. Kai saboda ganin wautar direbobin alli da yake, sai kawai ya kama rafka guda, wai shi ya yi naimijin kokari wajen fatatakar direbobin alli dubu kofar hanci.
Shi ke nan ’ya’yan talakawan Bawan-cici, kun samu rabo mai tsoka a romon Damo-da-kura-da-diyya. Kun ga alfanun Jinkiri da Jimirin cin jinbiri a dama-dama-da-kurda-kurdar siyasa, inda ake ta wasan Samson-siya-siya da kwakwalenku. Hakika Malam Ya-isa-Ya-yi-Guda. Sai rangada guda yake ta yi, wai daga cikin nasarorin da ya samu a shekarun da ya shafe yana jan ragamar mulkin Jihar Bakwon-cici, sun hada da toshe basirar ’ya’yan gama-garin al’umma, yanzu duhun jahala ya yi dimbin karuwa; za samu karin masu sara da adda da barandami.
A batu na waskiya, Gwamnan Jihar Bakwon-cici ya samu lambar yabo ta duniya, wajen Haramta Bobo da kwambon bokoko, ta yadda zai yi wuya nan gaba a sake samun kwararrun Bokayen Turai da msu jona-jiniya; da wuya asake yaye kwararrun direbobin alli. To abin da ya sa ya yi muku wannan gyaran gangar auzina shi ne, shi dai dan jam’iyya mai dan boto ne da sanda jirge, kuma kwararre ne a harkar jirgiya. Domin da mai dan boto da sanda jirge ta hana shi taka-kara, sai kawai ya yi saraf-na-sadaf, ya koma jam’iyya mai hoton masara, inda ya zama mugun dan masara!
Lallai Malam Ya-isa-Ya-yi-Guda! Irin wadannan ’yan gyare-gyare irin nag yare da kurege da ya aiwatar a Jihar Bawan-cici, na tabbata babu wani Gwamna-Gwaran-gwam a daukacin fadin Haurobiya day a taba samun irin wannan nasara. Ka da ba ku dauka ko ya yi laifi ne, a’a. Ai shugaban kasar Haurobiya ma yana fama da yajin aikin Jami’an Asusun Ilimi, wadanda ke koyar da watsattsake da buda wagagen littafai a cikin Jam’in Jama’a a Jami’o’i. To kun ji!
Direbobin alli, ku kara tyin na-damo, ku himatu ka’in da na’in wajen tarairayar ’yan makaranta masu kwazo, ku samar da gwaraza wajen za su yi wa mazaje kozo a lokacin tafiya Gwarzo. Ka da ku dora manyan gobe a tafarkin gurguwar hanyar karatun wasikar jakin-dawa da na gida, ta yadda za su yi wa al’umma wa-ka-ci-ka-tashi. Mun gaji da masu yi wa damin Hauron-Haurobiya kwashi-kwaraf. Abin takaici kuma shi ne, Loma-a-murde ya zama muzuru lami. Masu tukin alli dole ne ku bi da masu koyon watsattsake da buda wagagen litattafai labi mara kwazazzabo, don kada su tashi a karkatattacen tafarki, ta yadda idan sun shake lalitatrsu, to kowa ta shi, ta fisshe shi.
Batu na-ingarman karfe, wajibi ne Haurobiyawa su wancakalar da mulkin jam’iyya midan boto da sanda jirge, domin manufarta ta yi ta haifar da shagabannin al’umma irin su Gwamnan Bawan Cici, wanda ya tafka ta’asa, amma ya rika rangada guda kamar a gidan biki. Ko kuma ta samar muku da mutane irin su Baudadden Joji da masu yi wa tsofaffin ’yan kwadago fanco, ta hanyar wawashe kudin fensho.al’ummar Bawan-cici ku shata wa kanku alkiblar rayuwa, ta hanyar zabi-sonka, don kada ku sake zabo zabo mai tafka ta’asa ya yi ta guda wai ya yi aikin kwarai, alhali aiki kwarar jama’a ya yi. Mutanen Bawan-cici ku ari takalmin Malam Tunau, don zakulo abin da Malam Sa’adun Arewa ya yi tafafutika a kai. Idan ba ku je Gano ba, to sai in ce ku yi “Zungur, ka da ku yi Zugum!”

Sakonni:

Mazan kwarai
Assalamu alaikum yaku daliban wannan makaranta mai albarka ta Dodorido da fatan kowa ya tashi cikin uwar jiki lafiya a wannan rana babba. A yau kimanin shekara sili da tsayuwa bisa kafa daya da Dokta Mamma Shata uban  mawaka, dan mutan Jihar dakin kara  ya riga mu gidan gaskiya, Mai-duka ya kai rahama ga makwancinsa. Muna mika gaisuwa da ‘yar dugwi-dugwi ga marigayin dalibar makaranta Hajiya Halima Mai-duka ya kai ga makwancinsa amin. Daga Mai adana damin Hauro na jahar Bauchi, Auwalu yayan fati 08152073868 / 08120646429.

Direbobin alli
Bayan gaisuwa tare da jin jina ga DODO uban Dodanni. Ko gane mini hanya mahaukaci ya hau kura. Ina so al’umma su rika tunawa da girman da direbobin allin bokoko suke da shi, ba tare da an duba kwambon boko ko ba,  tunda ko a garin Ikko a kwambo. Domin a Jihar mu-muka-fara shari’a a daidai lokacin da ‘yan dugwi-dugwin talakawa za su kwankwadi romon damo-da-diya-kada, a daidai wannan lokaci sai ga shi ana nema a yi masu hannun jajirai, tunda su masu madafun iko suna da ikon tsallakar da ‘yan dugwi-dugwin su zuwa kasashen ketare, don su samu ilimin bokoko kuma su dawo suna su ci gaba daga inda iyayensu suka tsaya wannan ba sabon tsarin mulki ba ne a kasar Haurobiya ga shagabanninmu. Ina kira ga shagaban Jihar mu-muka-fara-shari’a Gwamnan talakawa dan mutan garin Talatar-fari. Tunda sanyin safiyar Talatar fari ya mai girma gwamna a  duba talakawan wannan jiha tamu. Daga: Jami’in hulda da jam’a na Jihar mu-muka-fara shari’a, Abdulnasir Lawal (ROCKY) 07035727178.

Fuskokin dalibai
Assalamu alaikum jama’a dama sauran daliban wannan makaranta mai albarka ta Dodorido. Ina kira ga dalibai wannan makaranta  muci gaba da jajircewa  wajen sada  zumunci a koda yaushe  don samun rahama  da samun falala mai albarka wajen mai duka. Domin sada zununci wani muhimmun abu ne a musulunci a fadar dan amina amincin mai duka ya isa gare  shi. Mai-duka ya  hada fuskokin mu a ranar babban taro da alheri. Daga dalibar makaranta Gimbiya Halima Shehu Shagamu 08038425171.

Taya murna
Bayan gaisuwa irinta masu fuskantar alkibla don gaida Mai duka Sili, ina jinjina ga ‘yan uwana daliban wannan makaranta ta Dodorido, da ma uban tafiya mallam DODO. A madadin daliban wannan makaranta tamu mai albarka, muna taya Babban Mutum Mai Rawani na Jihar Tumbin giwa cika shakara Babban lauje da zagaye akan karan gadon Jihar da kewayenta. Mai-duka ya taya shi riko ya sa ya gama lafiya. Daga daliban makarantar Tumbin giwa, Kwamared Nazifi Ubale 07036292681.   

Cigiya
Assalamu alaikum jama’a dama sauran daliban wannan makaranta mai albarka ta Dodorido. Ina cigiyar ‘uwa bada mama Hajiya Halima Mamman Shata (ANTI DUBU) . Duk wanda Mai-duka yasa suka yi na mujiya karamin lauje da iya, ya ce mata ‘yan dugwi-dugwi na kuka. Daga Mai adana damin Hauro na Jihar Bauchi, Auwalu yayan fati 08152073868 / 08120646429.