✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jihar Gombe za ta karrama kocin Eaglets Manu Garba

Majalisar Dokokin Jihar Gombe ta yi  kira ga gwamnatin jihar da ta karrama Kocin ’yan kwallon kafa na Golden Eaglet’s da ’yan wasan kungiyar da…

Majalisar Dokokin Jihar Gombe ta yi  kira ga gwamnatin jihar da ta karrama Kocin ’yan kwallon kafa na Golden Eaglet’s da ’yan wasan kungiyar da suka fito daga jihar wadanda suka samun nasara lashe kofin duniya na matasa a Dubai.
Haka kuma zauren majalisar ya yi kira ga gwamnatin da ta karrama dalibin da ya zama zakara na jarrabawar wannan shekara ta NECO daga makarantar Sakandaren al’umma ta garin Doho da ke karamar Hukuamar Kwami.
Shugaban kwamitin wasanni na majalisar Alhaji Ahmad Abubakar ne, ya mika wadannan roko biyu kuma nan take ya samu goyon baya da amincewar sauran mambobin majalisar.
A cewarsa yakamata ita kanta Makarantar Sakandaren al’ummar watau Doho Community Secondary School, a karramata saboda hakan zai karfafawa sauran makarantun da ke daukacin jihar gwiwa.
Shugaban kwamitin wasannin Alhaji Ahmad Abubakar, ya karfafa batun shirya liyafar karrama Kocin ‘yan wasan watau Manu Garba, kasancewarsa dan Gombe kuma ya yi namijin kokari wajen taka rawar da ta kai ‘yan wasan suka samu wannan gagarumar nasara.
Shi kuwa Kakakin Majalisar  Dokokin Alhaji Inuwa Garba, nuna farin cikinsa ya yi ga ‘yan asalin Jihar Gombe wadanda suka kara fitar da sunan jihar a idon duniya.
Daga nan sai ya bayyana samun nasarar ‘yan wasan na Golden Eaglets da cewa wata hanya ce ta kara samar da hadin kan kasa da dinke baraka.