✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jihar Nasarawa za ta ci gaba da ba fannin wasanni fifiko – Kwanta

Gwamnatin Jihar Nasarawa za ta ci gaba da ba fannin wasanni fifiko a shirye-shiryenta. Mai taimaka wa Gwamnan Jihar na Musamman a Fannin Matasa da…

Gwamnatin Jihar Nasarawa za ta ci gaba da ba fannin wasanni fifiko a shirye-shiryenta. Mai taimaka wa Gwamnan Jihar na Musamman a Fannin Matasa da Wasanni Mista Kwanta Yakubu ne ya bayyana haka a jawabinsa a wajen bikin ban-kwana da aka shirya wa ayarin kungiyar ’Yan Kwallon Kwando ta Jihar da aka gudanar a filin wasa na  Lafiya ranar Lahadin da ta gabata.

Ya ce gwamnatin Injiniya Abdullahi Sule ta gamsu da harkokin wasanni da  gagarumar gudunmawa da suke bayarwa wajen rage zaman banza da samar wa dimbin matasa ayyukan yi don dogara da kansu, inda ya ce babu shakka hakan yana rage wa gwamnati nauyi.

Ya ce da zuwan Gwamna Abdullahi Sule kan karagar mulki yake duk abin da ya kamata wajen inganta harkokin wasanni a jihar kuma hakan ya kai ga kungiyoyin wasan kwallon kafa na mata da na maza samun nasarar zama zakaru a gasar kasa da suka fafata kwanan nan. Ya bukaci ayarin ’yan wasan kwallon Kwandon wadanda za su wakilci jihar a gasar Kwallon Kwando ta Kasa karo na biyu a garin Ilorin a Jihar Kwara su tabbatar sun taka rawar da ta kamata wajen yin koyi da abin alfaharin da takwarorinsu na wasannin kwallon kafa a jihar suka yi wajen zama zakaru a karshen gasar don daukaka sunan jihar a fannin Kwallon Kwando.

Ya gode wa hukumomin manyan makarantun jihar wadanda a cewarsa sun taimaka matuka wajen samar wa kungiyar wasan  jihar da wasu daga cikin kwararrun ’yan wasansu don su wakilci Jihar Nasarwa a gasar.

Daga nan sai ya tabbatar wa ayarin cewa Gwamnatin Jihar Nasarawa za ta ci gaba da tallafa musu da duk abubuwan da suke bukata don cimma nasara.

Babban mai horar da ’yan wasan Kwallon Kwando ta Jihar, Abubakar Zico bayan ya yaba wa gwamnatin dangane da karamcin da ta yi musu, ya kuma yi alkawari cewa ba za su bai wa al’ummar jihar kunya ba. Ya ci gaba da cewa za su yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da sun yi nasara a gasar inda ya bukaci al’ummar jihar su ci gaba da ba su cikakken goyon baya don cimma nasara.