Search
Subscribe
Jihohi 26 da har yanzu ba su nada kwamishinoni ba

Jihohi 26 da har yanzu ba su nada kwamishinoni ba

Ba tare da wasu muhimmin dalilai ba, gwamnonin jihohi 26 daga cikin 29  da aka rantsar a ranar 29 ga Mayu wadanda har yau ba su kaddamar da majalisun zartarwa (kwamishinoni) ba, tare da cewa samar da su din wani yanki ne na abin da Kundin Tsarin Mulkin Kasa ya tanada.

Gwamnoni goma sha biyu ne sababbin kamu, 17 kuma sake zabarsu aka yi a zaben gwamnonin da ya gabata a ranar 9 ga Maris din bana. Makonni 8 bayan da suka sha rantsuwar kama aiki, wadanda kawai suka nada kwamishinoninsu  su ne Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal da na Kaduna Nasiru El-Rufa’i da Udom Emmanuel na Akwa-Ibom. Akwai karin wasu jihohi biyu da suka zabi kwamishinoninsu wato Jihar Legas da Jihar Binuwai. Amma sauran gwamnoni 24 sun rungume hannayensu ne kawai sun yi gum.

Gwamnan Jihar Katsina Aminu Masari shi ya zabi Kwamishina daya ne rak yayin da Gwamnan Ribas, Neysom Wike ya zabi guda biyu. Masari ya zabi Barista Ahmed El-Marzuk a matsayin Kwamishinan Shari’a. shi kuma Wike ya zabo Zachaus Adangor a matsayin Kwamishinan Shari’a da kuma Isaac Kamalu a matsayin Kwamishinan Kudi. Sannan ya zabo tsohon Ministan Wasanni Dokta Timi Danagogo a matsayin Sakataren Gwamnatin Jihar, da kuma Cif Chukwuemeka Woke a matsayin Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati. Yayin da shi kuma Gwamna Masari bai yi wani nadi ba tukuna.

Gwamna Samul Ortom na Jihar Binuwai da Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Jihar Legas sun tura da sunayen wadanda suka zabo a matsayin kwamishinoni zuwa ga majalisun jihohinsu don su samu amincewar majalsun. Sauran jihohin da har yanzu ba su zabo kwamishinonin ba sun hada da, Nasarawa, Gombe, Neja, Kebbi, Ogun, Bauchi, Imo, Zamfara, Kwara, Yobe, Enugu, Borno, Adamawa, Taraba, da kuma Kano. Haka kuma jihohin Jigawa da Kuros Ribas da Oyo da Ogun da Delta da Ebonyi da kuma Fulato har yanzu ba su da kwamishinoni.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya bayyana cewa ya jinkirta zaben kwamishinoninsa ne saboda yana son ya zabo sahihan mutanen da zai yi aiki da su a cikin shekara hudu masu zuwa. Mai magana da yawun Ganduje, Abba Anwar cewa ya yi “Mai girma Gwamna yana takatsan-tsan wajen zaben wadanda zai nada ne saboda gudun zaben tumun-dare.”

Abin da aka fi gani akasari yanzu shi ne, gwamnoni suna nada sakatarori da shugabannin ma’aikatan gidan gwamnati da kuma masu yin magana a madadinsu amma mafiya yawansu ba su nada ’yan majalisar zartaswa na jihohinsu ba. Mafi munin lamarin kuma yana a jihohin da su sam ma  ba su yi kowane rin nadi ba. Gwamnan Jihar Filato Samuel Bako Lalong da takwaransa na Jigawa Badaru Abubakar su har yau ba su yi nadi ba sam-sam duk kuwa da yake sake zabensu aka yi a karo na biyu. Amma ba tare da wata sanarwa a hukumance ba an ce Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa Abdulkadiri Fanini ya ci gaba da aikinsa.

Abin kunya ne ganin cewa kusan mako 5 da rantsar da su wato tun 29 ga watan Mayu har zuwa yau ba su samar da majalisun zartarwa ba a jihohinsu. Yayin da wadansu gwamnoni suka dauki nade-naden da muhimmanci wadansu kuma sun fara ne da yin kwantai. Duk wani Gwamna mai kishin zuci ya ci a ce ya fara tattara sunayen sahihan mutanen da zai yi aiki da su tun daga ranar da aka ce shi ne ya lashe zabe. Sannan akwai wajen wata biyu da aka share a tsakanin zaben da kuma rantsuwar kama aiki wannan lokaci ya ishi duk wani Gwamna mai tsinkaya ya shirya kuma ya rubuta tare da aika sunayen kwamishinoninsa zuwa ga Majalisar Jiharsa don su tantance su.

A maimakon ma su zauna a jihohinsu su yi aikin zabo kwamishinonin wadansu gwamnonin sun gwammace su taho Abuja su rashe na tsawon makonni. Wannan rashin nadin yana kuma shafar harkokin tattalin arziki, tunda duk Gwamnan da yake tsammanin shi kadai kwai zai iya tafiyar da harkokin mulkin jiharsa to kuwa yana yaudarar kansa ne kawai. Domin a matayin Babban Sakatare  na ma’aikacin gwamnati, ’yar gudumawar da zai bai wa Gwamna wajen awatar da burinsa ba ta taka kara ta karya ba.

Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, ya shardanta cewa daga lokaci zuwa lokaci ya dace Gwamna ya rinka zama tare da Majalisar Zartarwa ta Jiha don tattauna yadda za a ciyar da jama’ar jihar gaba. Don haka saboda kawo ci gaba da kuma kyakkyawan shugabanci muna kira ga duk wani Gwamnan wata jiha da bai riga ya kaddamar da Majalisar Zartarwar Jiharsa ba ya gaggauta yin haka ba tare da bata lokaci ba.

 

 

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin