✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jihohi biyar da ilimin mata ke ci baya a Arewa

Sarakuna sun nuna damuwarsu ka koma bayan ilimin yara mata a jihohi biyar na yankin.

Sarakuna a Arewacin Najeriya sun nuna damuwarsu game da mummunan halin da karatun yara mata ya shiga a jihohi biyar na yankin.

Sarakunan sun ce rashin tsaro, talauci, jahilci, da sauran kalubale na cikas ga ilimin yara mata a jihohin Borno, Zamfara, Gombe, Sokoto da Kebbi.

Sarkin Argungu da kuma Shugaban gidauniyar Sultan Foundation for Peace and Development, Mai Martaba Alhaji Samaila Mohammed Mera, ya ce “Muna da kalubale da yawa da suka sa yan matanmu suka daina zuwa makaranta wanda ya ya hada da jahilci, tattalin arziki, da rashin tsaro”.

Yayin kiran a zantawarsa da ’yan jarida a Kaduna bayan taron kwana 3 kan sanya yara mata a makaranta, sarkin ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su ci gaba zage damtse wurin yin kira zuga ga rungumar ilimin yara mata a yankin.

Ya ce taron ya tattauna “matsalar da ta sa matanmu ba su zuwa makaranta, da kuma abin da ke hana su kammala karatunsu”, da kuma hanyoyin tabbatar da cewa sun yi karatun domin amfanin al’umma.

“Borno ita ce jihar da tafi fama da matsalar saboda rashin tsaro, amma a nan muna da Zamfara, Gombe, Sokoto da Kebbi, wanda, a kididdiga ta nuna su ne suka fi lalacewa idan ana batun ilimin yara mata.

“Ran gadin da za mu yi nan gaba zai kasance zuwa kasar Habasha inda yara mata ’yan kalilan ne ke shiga makaranta”, inji sarkin.

Babbar mai fafutukar sanya yara mata a makaranta a Afirka, Dokta Mairo Mandara, ta ce an gudanar da wayar da kan ne domin tabbatar da cewa kowace yarinya ta kammala karatun sakandare.