Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Jihohi na ci gaba da gabatar da kasafin kudin badi

A ranar Litinin da ta gabata ce Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo ya mika wa Majalisar Dokokin jihar kasafin kudin badi  na Naira biliyan 118 da miliyan 737 da dubu 439 da 791.

Da yake mika kasafin kudin mai taken ‘Kasafin Kyakkyawar Makoma’ Gwamnan ya ce an yi haka ne don bunkasa tattalin arzikin jihar da ciyar da al’umma gaba. Ya ce an ware Naira biliyan 60.6 kan ayyukan yau da kullum, sai biliyan 58.1 kan manyan ayyuka.

ADVERTISEMENT

Haka Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong ya gabatar wa Majalisar Dokokin Jihar, kasafin kudin badi da jihar za ta kashe na Naira biliyan 148 da miliyan 700.

Da yake gabatar da kasafin, Gwamna Lalong ya ce an ware Naira biliyan 83 da miliyan 300 ga harkokin yau da kullum. Sai Naira biliyan 65 da miliyan 300 za su tafi ga ayyukan raya kasa.

ADVERTISEMENT

Ita ma Gwamnatin Jihar Borno za ta kashe Naira biliyan 125 da miliyan 82 a kasafin kudinta na badi. Da yake jawabi yayin mika kasafin ga Majalisar Dokokin Jihar, Gwamna Kashim Shettima ya bayyana cewa zai mayar da hankali ne wajen ci gaba da bunkasa harkokin rayuwar al’ummar jihar a daidai lokacin da suke farfadowa daga matsanaciyar wahalar rayuwa da Boko Haram ta jefa su a ciki. Ya ce za a kashe Naira biliyan 61 kan muhimman ayyuka, yayin da Naira biliyan 63 za su tafi wajen al’amuran yau da kullum.