✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jihohin da aka sanya dokar hana fita

Wasu jihohi sun sanya dokar hana fita bayan zanga-zangar ENDSARS ta kazance

Gwamnatin Jihar Imo ta sanya dokar hana fita ta tsawon sa’a 24 daga karfe 12 na dare ranar Talata a fadin jihar.

Gwaman Hope Uzodinma ya sanar da sanya dokar bayan rahotannin da ke cewa wasu bata-gari na neman fakewa da zanga-zangar ENDSARS su tayar da zaune tsaye a jihar.

Sanarwar da ya fitar ta ce sanya dokar hana walwalar ta zama wajibi kuma za ta ci gaba da aiki har sai abin da hali ya yi domin tabbatar da zaman lumana da jihar.

  • Dokar hana fita bayan kai wa Gwamnan Osun hari

Hakan na zuwa ne bayan takwaransa na Jihar Osun, Adegboyega Oyetola ya sanya dokar hana fita ta tsawon sa’a 24 a jiharsa.

Gwamna Oyetola ya ce dokar da za ta fara aiki daga karfe 12 na dare ta zama jazaman domin tabbatar da tsaro a jihar.

Idan ba a manta ba a ranar Lahadi masu zanga-zangar ENDSARS sun kai wa gwamnan hari a lokacin da ya je domin yi musu jawabi a garin Osogbo

  • Akeredolu ya sanya dokar hana fita a Ondo

A Jihar Ondo, Gwamna Arakunrin Oluwarotimi Akeredolu ya sanar sa makamanciyar dokar a wani sako da ta kafafen watsa labarai da ya ce ya yi ne domin kare rayukan jama’ar jihar, ciki har da matasa.

“Daga karfe tara na dare dokar za ta fara aiki sai abin da hali ya yi; Iyaye su tabbatar ‘ya’yansu sun zauna a gida”, inji shi.

Ya ce rahotannin barkewar rikici a wasu sassan jihar sun sa ya zama wajibi a dauki matakin domin tabbatar da doka da oda.

  • Ikpeazu ya wa Jihar dokar kulle

Gwamnan Abia, Okezie Ikpeazu ya sanya dokar hana fita na sa’a 12 bayan harin da aka kai wa ‘yan sanda a lokacin da suke sintiri a garin Aba.

Akalla ‘yan daba 30 ne suka far wa ‘yan sandan, suka kashe daya daga cikin jami’an suka kuma dauke makamansu.

  • Legas ta sanya dokar hana zirga-zirga

Tun da sanyin safiyar Talata Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Jihar Legas ya sanya dokar hana fita a Jihar bayan ‘yan daba da ‘yan kungiyar asiri sun saje da masu zanga-zangar har ta kai ga kashe mutum uku da safiyar ranar.

Rahotanni da almurun ranar Talata su ce sojoji sun bude wuta a kan masu zanga-zangar da suka yi tsinke a kofar birnin Legas da ke Lekki.

Jami’an tsaron sun bude wutar ne domin tarwatsa cincirindon masu zanga-zangar.

Bidiyon harbe-harben da masu zanga-zangar suka yada ya nuna sojojin na harbi.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun ce an kashe mutum daya wasu da dama kuma sun jikkata.

Masu zanga-zangar sun ci gaba da gangamin nasu ne duk da dokar kullen na awa 24 da gwamantin jihar ta sanya wanda ya fara aiki karfe 4 na yamma.

Suna tsaka da taron nasu a inda suka yi dandazon ne suka fara jin karar harbe-harbe, nan take wurin ya hautsine kowa ya yi ta kokarin neman tsira.

Rahotanni sun ce sojoji sun yi wa wasu daga cikin masu zanga-zangar kawanya bayan mutanen sun kekashe kasa cewa su ba za su watse ba.

A halin yanzu Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya dage lokacin farawar dokar da ya sanya zuwa karfe tara na daren ranar Talata.