✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jihohin Sakkwato da Katsina da Bauchi ne sahun gaba a kuncin rayuwa – UNDP

Mutanen jihohin  Sakkwato da Katsina da Bauchi da Yobe da kuma Zamfara su ne suka fama da kuncin rayuwa a tsakanin al’ummar Najeriya kamar yadda…

Mutanen jihohin  Sakkwato da Katsina da Bauchi da Yobe da kuma Zamfara su ne suka fama da kuncin rayuwa a tsakanin al’ummar Najeriya kamar yadda rahoton Ci gaban Al’umma na Kasa na bana wanda Hukumar Kula da Ci gaban Jama’a ta Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) ta sake ya nuna. An gina rahoton ne kan bayanan da aka tattara  a shekarar 2016.

Alkaluman da ke nuna ci gaban al’umma an takaita su ne kan fannoni uku na ci gaban jama’a da suka hada da: tsawon rai cikin koshin lafiya da damar samun ilimi da kuma rayuwa mai inganci.

A cewar Hukumar UNDP, ma’aunin HDI na wakiltar akasarin ma’aunan rayuwa ne da kowane daya daga cikin fannonin ke fadowa a karkashin fanonin nan uku na lafiya da ilimi da ingancin rayuwa.

Kuma jihohin da suka yi wa sauran jihohin kasar nan zarra a fannin ci gaban jama’a sun hada da: Legas da Abuja da Bayelsa da Akwa Ibom da kuma Ekiti.

Yayin da jihohin suka biyo bayansu suka hada da: Dalta da Kuros Ribas da Ogun da Ribas da Abiya da Enugu da Edo da Imo da Osun da Kwara da Nasarawa da Ondo, daAnambra da Filato da Benuwai da Taraba da Kogi da Oyo da Ebonyi da Adamawa da Kaduna da Gombe da Neja  daKebbi da Jigawa da kuma Kano.

Jihar Legas tana da darajar 0.6515 inda ta ci gaba da rike kambinta  ta daya a tsakanin jihohin kasar nan kamar yadda take a jadawalin shekarar 2013, inda ta samu darajar 0.6716.

Babban Birnin Tarayya, Abuja, ya zo na biyu da daraja 0.6289 inda ya tsallaka sama da matsayi  shida, daga matakin da yake kai a  shekarar 2013 da darajar 0.5112.

Jihar Bayelsa ce ta uku da darajar 0.5909 inda ta yi kasa daga matsayi na biyu a shekarar 2013 da darajar 0.6210.

Jihar Akwa Ibom ce ta hudu da darajar  0.5641, ta rike matsayinta na hudu kamar yadda take a baya da maki 0.5698.

Jihar Ekiti ce ta biyar da daraja ta 0.5608 kuma tana daya daga cikin jihohin suka yi gaba a kiyasin da aka yi, inda ta matsa da matsayi 11 daga matsayinta na 16 a shekarar 2013, yanzu matsayi take ta biyar.

Jihar Sakkwato ce ta farko a fagen kuncin rayuwa kuma ta karshe a jerin jihohin da suka yi kokarin inganta rayuwa da samar da ilimi da tsawon kwana da koshin lafiya a tsakanin jihohin kasar nan inda ta koma baya daga matsayi na 36 a shekarar 2013 zuwa matsayi na 37 a shekarar 2016 da daraja 01942 maimakondaraja  0.2910 a shekarar 2013.

Jihar Katsina ta gusa gaba da mataki hudu inda ta rike matsayi na 36 kuma ta biyu a koma-baya. Duk da haka kimarta ta karu daga 0.2364 a shekarar 2013 zuwa darajar 0.3031 a shekara 2016 na rahoton HDI.

Bauchi na da darajar 0.3238, inda take matsayi na 35 inda ta ci baya daga gurbinta na 29 a shekarar 2013 da darajar 0.2636.

Yobe, ce a matsayi na 34 da darajar 0.3249. a shekarar 2013,  ta cira sama daga matsayi na 37 da darajar  0.1247.

Jihar Borno ce a matsayi na 33 da darajar 0.3276; yayin da a shekarar 2013, take matsayi na 34 da darajar 0.2135.

Jihar Zamfara ce a matsayi na 32 da darajar 0.3392 ba kamar shekara uku da suka gabata da take matsayi na 30 da darajar 0.2623.

Rahoton na kasa ya gindaya a samu daraja 0.5114 akalla, sai dai jihohi 23 sun gaza cimma haka. Kuma adadin na shekarar 2013 ya tsaya ne a kan daraja akalla 0.5060.

Rahoton Ci gaban Jama’a na Kasa da aka fitar bana ya mayar da hankali ne kan inganta rayuwar jama’a  a yankin Arewa maso Gabas.

A yayin gabatar da rahoton a Abuja a Juma’ar da ta gabata  da dare, Ministan Kasafin Kudi da Tsare-Tsare, Sanata Udo Udoma ya ce, sakamakon magance matsalolin tattalin arziki da ci gaba a Arewa maso Gabas, kasar nan tana taimakawa wajen rage aukuwar ayyukan ta’addanci.

Ministan ya ce: “Wannan rahoto da ya fi mayar da hankali a kan yankin  Arewa maso Gabas ya tabbatar da cewa hare-haren Boko Haram na da alaka da fakewa da  addini ne sakamakon wasu matsalolin rayuwa da na tattalin arziki a Arewa maso Gabas.”

“Balo-balo rahoton ya tabbatar da dangantakar da ke tsakanin zargin rashin damawa da rashin adalci da kyama saboda addini da asarar dukiya da rashin aikin yi da rasa hanyoyin gudanar da rayuwa da rashin tsoma jama’a a muhimman sassa da suka hada da kiwon lafiya da ilimi da noma suna da alaka da rikici da tashin hankula a yankin Arewa maso Gabas na Najeriya,” inji shi.

Udoma ya kara da cewa, rahoton wani tuni ga matakan gwamnatoci da hukumomi da kungiyoyin bayar da tallafi da abokan Najeriya, cewa kasar nan tana bukatar bullo da hanyoyin rage abubuwan da suke kawo wa jama’a rashin ci gaba a Arewa maso Gabas.