✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jihohin Sakkwato da Katsina da Kebbi da Zamfara za su tallafa wa Jami’ar Usman dan Fodiyo

Gwamnonin jihohin Sakkwato da Katsina da Zamfara da Kebbi Aminu Waziri Tambuwal da Aminu Bello Masari da Abdul’aziz Yari Abubakar da Sanata Abubakar Atiku Bagudo…

Gwamnonin jihohin Sakkwato da Katsina da Zamfara da Kebbi Aminu Waziri Tambuwal da Aminu Bello Masari da Abdul’aziz Yari Abubakar da Sanata Abubakar Atiku Bagudo sun lashi takobin gabatar wa majalisun dokokinsu wani kudurin da zai ba su damar tallafa wa Jami’ar Usmanu dan Fodiyo da ke Sakkwato domin bayar da tasu gudunmawa wajen samar da kayan aiki ga jami’ar.
Gwamnonin wadanda suka yi jawabi a wurin taron liyafar da aka shirya tare da kaddamar da Gidauniyar Jami’ar don samar da isassun ofisoshin malamai da dakunan binciken kimiyya da na daukar darussa da dakunan kwanan dalibai da hanyoyi a cikin jami’ar.
A jawabin mai masaukin baki, Gwamna Aminu Tambuwal ya ce kafa Jami’ar Usmanu dan Fodiyo shekara 40 da suka gabata ya taimaka wa kasar nan wurin samar da kwararrun ma’aikata a fannoni daban-daban, ta hanyar samar da guraben karo ilimi mai zurfi a jami’ar.
Gwamna Tambuwal ya ce, “Kadan daga cikin dalilan da suka sa muke fuskantar yawan dalibai masu neman ilimi a jami’ar su ne, jami’ar na da kwararrun malamai wadanda za su iya gogayya da takwarorinsu da suke kasashe masu tasowa da wadanda suka ci gaba, kamar yadda tarihi ya nuna kuma muke ci gaba da gani. Wadannan abubuwa ne da suke zahiri kuma sun kasance mana abin alfahari duk in da muka samu kawunanmu.” Gwamnan ya bukaci jihohi su taimaka wa jami’ar a wannan lokacin da ya bayyana cewa ilimi ya shiga cikin mawuyacin hali na karancin kayan aiki. Ya ce duk taimakon da za su yi tunanin kamar suna yi wa Jami’ar Usmanu dan Fodiyo wa jama’ar jihohinsu suke yi. “Dalili duk shekara dubban kannenmu da ’ya’yanmu ke neman guraben karo ilimi a jami’o’in kasar nan. Duk wanda aka dauka yana neman ya samu ilimi a yanayin da ya dace, don haka wannan hakkin ya rataya ne a wuyanmu a matsayinmu na shugabanni,” inji shi.
Ya ce za su tuntubi abokan hadin gwiwa da suka hada da kamfanoni da manyan abokan arziki da suka yi karatu tare domin su je su yi nazarin wasu daga cikin muhimman abubuwan da jami’ar ke bukata don taimakwa kamar yadda wasu fitattun ’yan Najeriya suka fara aiwatarwa a shekarun da suka gabata.