Jinjina ga Gwamnatin Buhari da ta kaddamar

da jiragen kasa.

Ina so yin amfani da wannan damar ta jaridar Aminiya take ba mu, in jinjina wa Shugaba Muhammad Buhari a kan kaddamar da jiragen kasa na zamani, wanda za su rinka zirga-zirga tsakanin Kaduna zuwa Abuja. Gaskiya kaddamar da jiragen yana da mutukar mahimmanci ga al’ummar Najeriya, saboda talakawa za su samu saukin tafiye-tafiye, tunda jirage ne na zamani masu mutukar gudu, da kuma dadi. Kuma kudin da talaka zai biya yana da sauki. Don haka ya kamata Shugaba Muhammad Buhari ya yi kokari ya kaddamar da irin wadannan jirage a dukkan manyan hanyoyin Najeriya, saboda irin muhimmancin da jiragen suke  da shi a fannin sufuri. Kuma samar da su din zai tallafa wa tattalin arzikin Najeriya.

Daga Muhammad Babangida Kiraji, Gashua, 08029388699. babangida30@yahoo.com

ADVERTISEMENT
Share