Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Jinjina ga uwar marayun Kaduna

Jinjina ga uwar marayun Kaduna

A yau na shigo wannan fili domin jinjina ga uwar marayu, wadda har masu uwar ma ba ta bari ba. Wato Shugabar Gidauniyar Centre for Charity and Debelopment of Women and Children in Africa.

A makon jiya ne na ji ana bikin murnar ranar haihuwarta, na ga yadda mutane suke ta gogoriyo wajen taya ta murna, suna sam-barka da yi mata fatar alheri, sai abin ya ban sha’awa.

Hajiya Binta Abdullahi Kowa mace mai tausayi da hakuri da sanin ya kamata musamman wajen taimakon al’umma domin ba ta so ta ga mutum ya shiga halin kunci ko damuwa. Tana taimakon  marasa galihu da mata musamman na karkara da birane.

Ta tallafi marayu ta hanyar tufatar da su da ciyar da su da daukar nauyin karatunsu da sama  musu sana’o’i ta yadda za su dogara da kansu. Wannan ya sa ake yi mata lakabi da uwar marayu.

Haka kuma duk inda ta ji labarin wani rashin adalci da aka yi wa wani ko wata, takan tsaya kai da fata a karkashin wannan kungiya tata ta ga an sama wa wannan mutum hakkinsa. Ta karkashin wannan kungiya Hajiya Binta ta koya wa mata sana’o’i don dogaro da kansu a gidan mazansu, kamar hada sabulu da man shafawa da man wanke kai da turaren kanshi da saka da dinki.

Matasa ba ta bar su a baya ba don su ma an tallafe su ta yadda za su dogaro da kansu ta hanyoyi da yawa. A takaice dai Hajiya Binta uwa ce ga al’umma masu galihu da marasa galihu.

Muna addu’a Allah Ya wa rayuwarta albarka, ya biya mata dukkan bukatunta na alheri duniya da Lahira.

Wani babban al’amari da ta yi ta kuma burge mutane sosai, shi ne yadda aka samu wata mata a cikin garin Hayin Dogo da ke Samarun Zariya a Jihar Kaduna ta haifi yarinya mace amma ita mahaifiyar ba ta da lafiya tana fama da ciwon kansar mama, nan take Hajiya Binta Abdullahi Kowa ta dauki nauyin matar da yarinyar inda ta yi alkawarin za ta rika biya musu dukkan bukatunsu na yau da kullum har Allah Ya ba mahaifiyar lafiya. Wannan abin a wannan lokacin ya samu karbuwa matuka, kuma ya bi gari sosai inda aka rika sambarka. A karshe, yadda Hajiya ke taimakon al’umma, muna addu’ar ita ma Allah Ya dafa mata.

Daga Ahmad Rufa’i Shu’aibu, Majidadin Sadaukin Zazzau, (08036861137)