✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jirgin soji ya ragargaji kwamandojin Boko Haram a Borno

Rundunar sojin sama ta Najeriya ta ce  ta ragargaza kwamandojin kungiyar Boko Haram da sansaninsu a jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin kasar. Kwadinatan…

Rundunar sojin sama ta Najeriya ta ce  ta ragargaza kwamandojin kungiyar Boko Haram da sansaninsu a jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin kasar.

Kwadinatan Rudunar na bangaren watsa labarai, Manjo Janar John Enenche ya ce jirgin yakin ya yi luguden wuta a kebabben mazaunin jagororin Boko Haram da sauran wuraren da ke zagaye da shi.

Sanarwar da ya fitar a ranar Juma’a ta ce an kai farmakin ne ranar 17 ga watan Yuni bayan an dade ana tattara bayanan sirri da leken asirin matattarar ‘yan kungiyar.

Enenche ya ce, a yayin leken asiri da rundunar ta gudanar ta gano dandazon ‘yan Boko Haram da sansaninsu da kuma wani gida da ake tsammanin daga nan suke shirya ta’adancinsu a yankin.

Ya kara da cewa jirgin yakin sojin saman Najeriya na “Operation Long Reach”, na dakile shugabannin Boko Haram a Arewa maso gabas ne ya yi luguden wuta a wuri inda ya ragargaza maboyar ‘yan kungiyar.