✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jiragen yakin Siriya sun kai hari kan motocin sojojin Turkiyya

Jiragen yakin kasar Siriya, sun kai hari a kan wani ayarin motocin sojojin Turkiyya da suka ketara zuwa cikin Siriya, lamarin da ya kai ga…

Jiragen yakin kasar Siriya, sun kai hari a kan wani ayarin motocin sojojin Turkiyya da suka ketara zuwa cikin Siriya, lamarin da ya kai ga rasa rayuka da kuma jikkata wadansu da dama.

Tuni kasar Turkiyya ta yi Allah wadai da faruwar haka, ta ce harin ya yi sanadiyar mutuwar farar hula uku, baya ga raunata wadansu 12.

Wani hoton bidiyo ya nuna yadda jiragen yakin Siriya ke auna ayarin motocin sojojin Turkiyya, yayin da ya doshi garin Sarakeb da ke Arewacin Idlib.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Siriya ta koka kan yadda sojojin Turkiyya ke shiga kasarta ba tare da izini ba.

Gidan talabijin din Gwamnatin Siriya ya yi zargin cewa ayarin motocin sojin na dauke ne da wasu kayan yaki don bai wa kungiyoyin ta’adda da ke yakar Gwamnatin Siriya a wajen garin Khan Sheikhoun mai muhimmanci.