Da Dumi Dumi

Jirgin mahajjatan Bauchi ya baro Alhazai biyu a Saudiyya

Mukaddashin sakataren cibiyar Hukumar Jindadin Alhazan Najeriya ta jihar Bauchi, Alhaji Kasim Danlami,  ya bayyana cewa, an baro alhazai biyu na jihar a kasar Saudiyya inda suke yin jinya sakamakon rashin lafiya da suke fama da ita.

Alhaji Kasim, ya bayyana hakan ne a filin jirgin saman Sir Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, bayan kammala jigilar dawo da alhazan jihar na bana zuwa gida.

Jirgin saman karshe na dawo da mahajjatan Bauchi na kamfanin Max Air ya sauka ne da misalin karfe 4:00 na asuba dauke da alhazai 281.

Share