✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jirgin sama ya dira a kan titin mota

Wani jirgin saman fasinja a Iran ya kaucewa hanyarsa ta sauka inda ya dira a kan titin mota. Biyu daga cikin fasinjoji 136 da ke…

Wani jirgin saman fasinja a Iran ya kaucewa hanyarsa ta sauka inda ya dira a kan titin mota.

Biyu daga cikin fasinjoji 136 da ke cikin jirgin sun samu rauni a kafa a hadarin wanda ya faru a birnin Mahshahr, kamar yadda likitoci suka bayyana.

Jirgin na Caspian Airlines sanfurin McDonnell Douglas MD-83 ya taso ne daga birnin Tehran.

Gidan talbijin na kasar ya ambato jami’an yankin na cewa matukin jirgin ne “ya yi jinkiri wurin sauka abin da ya ya kaucewa titinsa”.

Mohammad Reza Rezaei ya kara da cewa wannan ne “ya sa jirgin ya zarce hanya sannan ya dira a wani wuri” da ke kusa da filin saukar jiragen.