✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jirgin saman Ethiopian Airlines ya yi hadari da fasinjoji 157

Rahotanni na bayyana cewa, jirgin saman kamfanin Ethiopian Airlines Boeing 737 ya yi hadari a kan hanyarsa daga birnin Addis Ababa zuwa Nairobi babban birnin…

Rahotanni na bayyana cewa, jirgin saman kamfanin Ethiopian Airlines Boeing 737 ya yi hadari a kan hanyarsa daga birnin Addis Ababa zuwa Nairobi babban birnin Kenya da fasinjoji 157.

Hadarin ya faru ne da misalin karfe 08:44 na safe agogon can a yau Lahadi, jim kadan bayan da ya tashi daga babban birnin kasar Ethiopia.

A wata sanarwa da kamfanin ya fitar ya ce za a fara aikin ceto, sai dai ya ce ba a san adadin mutanen da hadarin ya rutsa da su ba tukuna.