Da Dumi Dumi

Jirgin saman Ukraine dauke da fasinjoji 176 ya yi hatsari a Iran

Jirgin saman Ukraine

Rahotanni na bayyana cewa jirgin saman Ukraine da ya yi hatsari a Iran na dauke da fasinjoji 176 duk sun mutu a cikin jirgin akwai ‘yan kasar Iran 82 da suka mutu.

Jirgin saman ya bai dade da tashi daga birnin Tehran ba a jiya Laraba, kamar yadda kafar sadarwa ta kasar Iran ta sanar.

Ofishin jakadancin Ukraine da ke Tehran ya bayyana cewa matsalar inji ce ta yi sanadiyar hatsarin jirgin ba wai harin ta’addanci ba.

Kafar sadarwa ta IRNA, ta ce, cikin wadanda suka mutu fasinjoji 167 ne sannan ma’aikatan jirgin 9 da ke aiki da kamfanin jirgin saman Ukraine International Airlines.

ADVERTISEMENT
Share