✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jita-jita ta sa ’yan Acaba sun auka wa ’yan KASTLEA a Zariya

A ranar Larabar makon jiya ne dubban ’yan Acaba  masu haya da babura suka  gudanar da zanga-zanga a  Zariya har zuwa fadar Mai martaba Sarkin…

A ranar Larabar makon jiya ne dubban ’yan Acaba  masu haya da babura suka  gudanar da zanga-zanga a  Zariya har zuwa fadar Mai martaba Sarkin Zazzau suna zargin ma’aikatan Hukumar Kula da Ababen Hawa da Tsabtace gari ta Jihar Kaduna (KASTLEA) da kashe musu abokin aiki.

Zanga-zangar wadda ta so ta ta da hakalin al’ummar  Zariya, a lokacin an rika yada jita-jitar cewa jami’an KASTLEA sun bi wani mai haya da babur  mai suna Isiya Salisu Rafin Yashi sun  taka shi da mota ya rasu.

Mai martaba Sarkin Sazzau Alhaji Shehu Idris ya yi zama da wakilan  masu haya da baburan, tare da Shugaban Karamar Hukumar Zariya Alhaji Idris Aliyu da Jami’in  ’Yan sanda (DPO) mai na yankin Zariya, inda    Sarkin ya ba ’yan acaban hakuri, tare da  nada kwamiti domin gano yadda lamarin ya faru.

Sai dai daga baya fasinjan da marigayi dan acabar ya dauko, mai suna  Ibrahim Habib da ke zaune a Unguwar Kaura a cikin Zariya ya yi wa Aminiya karin haske cewa: “Dan acabar ya dauko ni ne daga Titin Park Road da ke Sabon Gari zuwa Unguwar Low-Cost a cikin Zariya. Bayan mun fito daga Kofar Doka sai muka yi kicibis da ’yan KASTLEA suna tafiya. To a gaskiya mai babur din yana gudun da ya wuce kima.  Mun isa wata kwana, yayin da muke kokarin wuce motar ’yan KASTLEA ta dama a daidai lokacin motarsu tana kokarin yin kwana, shi ne muke gogi motarsu muka fadi.”
Ya kara da cewa:  “Na fadi gefe daya, dan acabar ya fadi a daya gefen titin kuma kafin a ce kwabo wata mota da ke guje ta taka masa kai. Nan take ’yan KASTELA suka kwashe mu zuwa Asibitin Wusasa aka yi mini allurai aka ba ni magunguna yayin da aka ce a wuce da dan acabar zuwa Asibitin Shika.  Gaskiyar magana ba ’yan KASTELA ne suka taka shi ba, sun taimake mu ne wajen kai mu asibiti, mutane ne kawai suke yada jita-jita.”

Wani wanda hadarin ya faru a gabansa  mai suna Abubakar Sani ya ce, “A gaskiya dan acabar ne ya zo a guje da yake akwai karar kwana sai ya buga wa ’yan KASTLEA, sun dauke shi ne zuwa asibiti amma kafin ka ce haka ’yan acaba kusan dubu sun taru suna ta jifar ofishinsu sai da ’yan KASTLEA suka rika tube kayan aikinsu suna shiga cikin mutane domin su tsira kada a kashe  ko a raunata su.”

Shugaban Hukumar KASTLEA  mai kula da Shiyya ta 6 da  7, Alhaji Salisu Magaji Muhammed ya musanta rahotannin da ake yadawa cewa ma’aikatansu ne suka jawo rasuwar dan acabar, inda ya ce, “Bayanan da ake yadawa a farko ba haka abin yake ba.  Motarmu wadda take zuwa aiki za ta shiga karamin ofishimu da ke kusa da Asibitin Dabbobi daidai kwanar sai wani dan acaba ya zo ta bayansu da gudu ya bi ta hannun dama  inda za su juya sai ya bugi gefensu har ya karya musu mudubin gefen dama sai babur din ya juya shi kuma ya fadi a gefen da masu shigowa zuwa cikin garin  Zariya suke bi, to motoci na wucewa sai wata ta taka shi. Nan da nan mutanenmu suka dauke shi zuwa Asibitin Wusasa daga nan aka wuce da shi zuwa Asibintin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika Zariya. Lokacin da muka kai shi yana magana, mu ne muka dauki nauyin kula da shi tunda yana cikin aikinmu karewa da taimaka wa masu hadari.To muna  dawowa daga asibitin ne sai muka samu labarin ’yan acaba suna baza labarin cewa ’yan KASTLEA  sun kashe wani kuma sun taka wata mata wanda gaskiyar al’amari  ba haka  abin yake ba.”

Malam Salisu Magaji ya nemi ’yan acaba da sauran al’umma su rika gudanar da bincike kafin daukar kowane irin mataki. Ya ce da yawa daga cikin ’yan acabar da ke tuka babur a Zariya ba su san ka’idar tuki ba wanda hakan ya sa kullum ake yawan samun hadurra.

DPO Kasim Abdul ya tabbatar da aukuwar lamarin,  inda ya ce tuni rundunarsa ta gano sunan mai babur din wato Isiya Salisu Rafin Yashi da ke Karamar Hukumar Zariya. Ya ce tuni ’yan uwansa suka dauki gawarsa inda aka yi masa sutura.