✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…JNI kuma ta shirya atisaye ga ’ya’yanta

Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) a Jihar Gombe ta gudanar da atisaye don horar da ’yan agajinta sanin makamar aiki. Da yake jawabi a lokacin…

Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) a Jihar Gombe ta gudanar da atisaye don horar da ’yan agajinta sanin makamar aiki.

Da yake jawabi a lokacin rufe taron da ya gudana a Kwalejin Larabci ta Gwamnati (ATC) da ke Gombe, Gwamnan Jihar, Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya, ya karfafa wa Kungiyar JNI kan shirya wannan taro ga ’yan agajinta, inda ya ce hakan ne zai ba su damar fuskanatar kalubalen zamani a kan aikin.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin mai ba shi shawara kan hulda da jama’a, Dokta Auwal Abdullahi Gafakan Akko, ya jinjina wa ’yan agajin kan yadda suka fuskanci wannan atisaye.

Gwamnan ya hore su da su yi aiki da abin da suka koya a wajen bada horon don ya amfane su da sauran mambobin kungiyar baki daya.

Da yake jawabi, Mai martaba Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III, ya bada tabbacin karin goyon baya ga Kungiyar JNI.

Sarkin wanda ya samu wakikcin Babban Sakataren Kungiyar ta Kasa, Alhaji Saleh Damburam Magajin Malam na Gombe, ya bayyana aikin agaji a matsayin hanyar hidima ga al’umma sannan ya kiraye su da su zama masu hakuri yayin gudanar da aikinsu.

Uban Kungiyar ta Jiha, Mai Kaltungo, Injiniya Saleh Muhammad, gode wa Gwamnan Jihar ya yi kan yadda yake bai wa kungiyar goyon baya ya kuma tunatar da Gwamnan cewa gwamnatin da ta gabata ta yi musu alkawarin Naira miliyan 10 don gina sakatariyar kungiyar; amma har ta kau kudin ba su iso ba.

Alhaji Bappaji Abubakar, Shugaban Kungiyar ta Jihar Gombe, ya ce kungiyar ta gudanar da bitar ce domin fadakar da mambobinta aikace- aikacen da ta sa a gaba.

Shugaban wanda ya yi magana ta bakin Sakatarensa, Isah Galadima, ya ce kimanin mambobi 500 ne suka halarci atisayen daga daukacin kananan hukumomin jihar 11.