✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

John Terry yana son zama Kocin Newcastle

Tsohon Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da ke Ingila, John Terry ya shiga sahun wadanda ke zawarcin zama Kocin kulob din Newcastle United…

Tsohon Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da ke Ingila, John Terry ya shiga sahun wadanda ke zawarcin zama Kocin kulob din Newcastle United da ke Ingila. Terry wanda a yanzu shi ne Mataimakin Koci a kulob din Aston Billa ya yanke shawarar ya nemi horar da kulob din Newcastle ne bayan kocinsu Rafael Benitez ya ajiye aiki.

Daga cikin wadanda suke zawarcin zama Kocin Newcastle din har da tsohon dan kwallon Arsenal, Mikel Arteta da yanzu haka yake Mataimakin Kocin Manchester City.

Rahoton da jaridar The Sun ta Ingila ta kalato, ya nuna John Terry dan kimanin shekara 38 shi ne na biyu a jerin wadanda ake ganin sun fi cancantar horar da kulob din Newcastle.  Wanda ake hasashen ya fi Terry cancanta shi ne Mikel Arteta.

Idan Terry ya zama koci, zai bi sahun takwaransa Frank Lampard da suka yi wasa tare wanda ya zama sabon kocin Chelsea a makon jiya.