✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Johnny Depp na shirin barin harkar fim

dan fim din Amurka, wanda ya saba fitowa cikin fina-finan yaki da na al’ajabi, Johnny Depp ya tada kabbarar ban kwana da sana’ar fim.dan wasan…

Johnny Depp, mai shirin ritaya daga fimdan fim din Amurka, wanda ya saba fitowa cikin fina-finan yaki da na al’ajabi, Johnny Depp ya tada kabbarar ban kwana da sana’ar fim.
dan wasan wanda fim dinsa na kwanan nan, ‘The Lone Ranger’ ya fara tada kura, ya fara sanun cece-kuce daga manazarta fina-finai na duniya. Johny ya fito a fim din a matsayin mayaki dan Amurka.
Da yake bayyana shirinsa na barin sana’ar fim, ya bayyana cewa: “Zama jarumi a fim wani abu ne mai kama da hauka-hauka, ba kowa ne zai iya jurewa ba.”
dan wasan, dan shekara 50 da haihuwa, ya ce ba yanzu-yanzu zai dakatar da kansa daga sana’ar ta fim ba, amma dai ya bayar da tabbacin cewa, zai yi haka ba nan da nisa ba.
A yayin tattaunawarsa da BBC, ya ambata cewa kafin ya tarkata komatsansa ya bar sana’ar fim, zai sake fitowa a fim din ‘Pirates of the Caribbean’ a matsayin Captain Jack Sparrow.
dan wasan dai ya yi suna sosai, musamman saboda yanayin fina-finansa na jaruntaka. Ya samu kyaututtukan yabawa na Oscar har sau uku.