✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jonas Sabimbi: An sake binne tsohon shugaban ’yan tawayen Unita a Angola bayan shekara 17

An sake binne tsohon shugaban ’yan tawayen Unita a kasar Angola, Jonas sabimbi, shekara 17 bayan mutuwarsa. Dubban tsoffin mayakan Unita sanye da riguna masu…

An sake binne tsohon shugaban ’yan tawayen Unita a kasar Angola, Jonas sabimbi, shekara 17 bayan mutuwarsa.

Dubban tsoffin mayakan Unita sanye da riguna masu dauke da hoton Mista Sabimbi, sun halarci bukukuwan sake binne shi wanda aka yi a kauyensa mai suna Lopitanga.

Mutuwarsa a shekarar 2002 ya kawo karshen daya daga cikin munanan yakin basasa da aka shaida a nahiyar Afirka.

An hannuntawa iyalan Mista Sabimbi gawarsa, a makon jiya, biyo bayan rudanin da aka samu a farkon makon.

Kungiyar Unita, ta ce bukin sake bizne shugaban nata, wani muhimmin mataki ne ta fuskar sasanta zaman lafiya a kasar ta Angola mai dan karen arzikin man fetur.

Sai dai kamfanin dillancin labaran AFP, ya ruwaito babu wani jam’in gwamnatin kasar ko daya da ya halarci bukin sake bizne Sabimbi.

An dai lullube makarar da ke dauke da gawarsa da tutar kungiyar Unita, mai launin kore da kuma ja.

Kasar Angola a baya, ta zama kasar da ake yakin cacar baka a kanta, yayin da Amurka da kuma gwamnatin wariyar launin fatan Afirka ta Kudu ke goyon bayan kungiyar ’yan tawayen Unita, a gefe guda kuma jam’iya mai mulki kasar ke samun mara baya daga gwamnatocin tsohuwar rusasshiyar Sobiyet da kuma Cuba.

An dai kiyasta mutune akalla dubu 500 ne suka rasa rayukansu, a yakin basasar da aka shafe shekaru 27 ana gwabzawa.

Durao Sakaita, daya daga cikin manyan ’yayansa, ya gayawa wata kafar labaran kasar cewa, iyalan Sabimbin za su sami sararawa daga karshe, bayan an sake bunne shi.

Bayanai akan Sabimbi a takaice:

An masa lakabi da suna ‘bakin zakara’ kuma ya kasance wani jigo mai matukar bijirewa

An zarge shi da kitsa munanan ababuwa, kuma ya kasance jagoran da dubban mutane ke girmamawa.

Dakarun gwamnati ne suka hallaka a shekarar 2002, an kuma bunne cikin gaggawa a wata makabarta dake tsakiyar garin Luena.

Za a sake kabarce shi ne kusa da kabarin mahaifinsa.

Iyalansa da kuma kungirsa sun nemi da sake masa kabari shekaru da dama: amma hakan bai samu ba.

An warware kiki-kakar ne bayan da tsohon abokin gabarsa, Jose Eduardo Dos Santos, yayi murabus daga kujerar shugabanci a shekarar 2017.

Sai dai sabon shugaban kasar, Joao Lourenco, ya amince da bukatar sake wa Sabimbin kabari; an kuma tona kabarin a farkon shekarar nan, bayan gwajin kwayoyin halitta sun tabbatar da cewa shi ne.

Ya kafa kungiyar Unita a shekarar 1966 a gabashin Angola

Ya ajiye karatunsa na aikin likita a kasar Portugal, inda ya shiga gwagwarmayar yaki da mulkin mallaka

Duk da samun yanci kasar Angola a shekarar 1975, kungiyar Unita ta cigaba da yakar gwamnati

Ya samu goyon bayan gaske daga kasar Amurka; sannan ya gana da shugaba Reagan a fadar White House a shekarar

An yi murna da mutuwarsa a shekarar 2002, a birnin Luanda, babban birnin kasar