✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jonathan, Buhari sun kashe Naira tiriliyan 1.164 a wutar lantarki

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kashe sama da Naira tiriliyan 4.7 a fannin wutar lantarki daga shekarar 1999 zuwa 2010, amma har yanzu kasar na zama…

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kashe sama da Naira tiriliyan 4.7 a fannin wutar lantarki daga shekarar 1999 zuwa 2010, amma har yanzu kasar na zama cikin duhu.

A cikin shekara takwas lokacin mulkin Jonathan da Buhari an sake zuba wasu kudade da suka kai Naira tiriliyan 1.164, duk da haka a yanzu haka masana’antu da gidajen jama’a ba su samun isashhen wutar lantarki.

John Ogbor mai shekara 45, wanda dan asalin garin Igedi a karamar hukunar Obi da ke jihar Benuwe, ya ce a yanzu haka yana zaune a unguwar Moro da ke hanyar Shagamu zuwa Ikorodu a jihar Ogun sama da shekara 14 a unguwar, bayan ya bar garinsa na asali ya ce sama da shekara bakwai yana zaune ba wutar lantarki a yankin.