✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jonathan ya bukaci a bunkasa harkokin inshora da Takaful a Najeriya

Shugaba Jonathan ya yi alkawarin ganin Gwamnatin Tarayya ta tallafa wa wajen ganin an bunkasa harkokin inshora a Najeriya. A cewarsa, akwai shirin fadada harkokin…

Shugaba Jonathan ya yi alkawarin ganin Gwamnatin Tarayya ta tallafa wa wajen ganin an bunkasa harkokin inshora a Najeriya. A cewarsa, akwai shirin fadada harkokin inshora da tsarin Musulunci na Takataful.
Shugaban ya yi wannan bayanin ne a lokacin da aka karrama shi da lambar yabo ta cibiyar Kula da Harkokin Inshora a Afirka ta Yamma (WAII), a Abuja.
“Wannan tsari ya yi daidai da manufarmu ta kawo sauyi, musamman wajen inganta tsarin inshora a harkokin tattalin arzikin Najeriya, don haka muke da zimmar bunkasa kannanan tsarin inshora da Takaful. Burin gwamnatin nan ne ta ga cewa wannan yunkuri da muka yi ya kawo ci gaba harkokin inshora a wajen hada-hadar harkokin kasuwanci,” inji shi.
“Wannan gwamnati na sane da cewas harkar inshore babban al’amari ne wajen bunkasa tattalin arziki ga kowace kasa. Muna daukar inshora da kima, don haka kamfanonin inshore a Najeriya ke bayar da muhimmiyar gudunmuwa ga tattalin rayuwarmu. Wannan gwamnati ta fito da tsare-tsare bunkasa kamfanonin inshore a kasar nan. Kuma wannan a bayyane yake a karkashin shirin Inshorar rayuwa ta Group Life Insurance Policy, inda gwmanatin tarayya ta fito a sahun gaba, wajen ganin daukacin ma’aikatanta da kaddarorinta an yi musu inshora,” a cewarsa.
Ya ce, akwai shirin da ake gudanarwa da nufin daidaita matsayin ayyukan inshore, ta yadda za su yi kafada da kafada da na sauran kasashen duniya, wajen bayar da kariyar asara ga masu mu’amala da inshore a Najeriya. Kuma a cewarsa, “sayar da kadarori da sakin haja ta samar wa kanta kimar daraja a kasuwa, shiri ne na gwamnati da zai bunkasa kamfanoni masu zaman kansu.
Ya karkare jawabinsa, tare da nuna farin cikinsa, kan yadda gwamnati ta juya akalar harkokinta daga kamfanonin inshora biyu mallakar gwamna da a da take amfani da su.