✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jonathan ya kori ministoci tara •Babu siyasa a ciki – Maku

Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya kori ministoci tara daga gwamnatinsa a shekaranjiya Laraba. Shugaba Jonathan ya bayyana haka ne a lokacin taron Majalisar Zartarwarsa…

Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya kori ministoci tara daga gwamnatinsa a shekaranjiya Laraba. Shugaba Jonathan ya bayyana haka ne a lokacin taron Majalisar Zartarwarsa na mako-mako.
Ministocin da korar ta shafa sun hada da Ministan Harkokin kasashen Waje da na Ilimi da na Tsare-Tsaren kasa da na Muhalli da na Gidaje da kuma na Kimiyya wato Ambasada Olugbenga Ashiru da Farfesa Rukayyat Rufa’i da Dokta Shamsudeen Usman da Hajiya Hadiza Ibrahim Malafiya, da Mis Amma Pepple da kuma Ita Oko Bassey.
Sauran su ne Minista a Ma’aikatar Tsaro da takwararta ta Wutar Lantarki da na Aikin Gona Misis Erelu Olushola Obada da Hajiya Zainab Kutchi da kuma Alhaji Bukar Tijani.
Da yake karin bayani ga manema labarai bayan taron majalisar Ministan Watsa Labarai Mista Labaran Maku ya bayyana sauke ministocin a matsayin kwarya-kwaryar gyaran fuska, inda ya ce “abu ne da ake yi lokaci-lokaci.”
Mista Maku ya ce Shugaban kasar ya salami ministocin ne domin “Ya sake alkiblar gwamnati ta wajen sanya sababbin jini, a shirin sake fasali na gwamnatinsa domin tabbatar da ingantaccen aiki ga jama’a.
Ya ce, Jonathan ya tabbatar wa korarrun ministocin cewa za su ci gaba da amfani ga shirin gwamnatinsa na sake fasalin kasa.
Maku ya ce kafin nada sababbin ministoci Sakataren Gwamnatin Tarayya Anyim Pius Anyim bisa umarnin Shugaban kasa ya umarce shi (Maku) ya kula da Ma’aikatar Tsaro; sai Minista na daya a Ma’aikatar kasashen Waje Farfesa  biola Owulere ya kula da Ma’aikatar Harkokin Waje, sai Minista a Ma’aikatar Ilimi Nelsom Wike ya kula da ma’aikatar, yayin da Minista a Ma’aikatar Harkokin Neja-Delta, Gayius Dahiru zai lura da Ma’aikatar Muhalli, sai Ministan Albarkatun kasa Musa Sada zai kula da Ma’aikatar  kasa, Gidaje da Rayya Birane.
Mista Maku ya kara da cewa Ministar Kimiyyar Sadarwa Misis Omobola Johnson za ta kula da Ma’aikatar Kimiyya da kere-kere, sai Minista a Ma’aikatar Ayyuka Ambasada Bashir Yuguda zai lura da Ma’aikatar Tsare-Tsare, sai Ministan Wutar Lantarki Farfesa Chinedu Nebo da takwararsa na Aikin Gonad a Raya Karkara Dokta Akinwumi Adesina za su kula da daukacin harkokin ma’aikatunsu zuwa lokacin da za a nada ministoci a ma’aikatun.
Minista Maku ya ce Shugaban kasa zai mika wa Majalisar Dokoki ta kasa jerin sunayen wadanda za su maye gurbin ministocin da aka kora domin neman amincewarta.
Ya ce, ministocin da abin ya shafa Shugaban kasar ya nuna gamsuwarsa da jin dadi kan sadaukar da kansu ga gwamnati tun lokacin da aka nada su. “Kuma ya gode musu kan aikin da suka yi wa kasarsu, inda ya ce zai ci gaba da tuntubarsu ta wasu hanyoyin domin aiwatar da shirinsa na sake fasalin kasa da kuma sauran al’amuran da suke kalubalantar kasar nan,” inji shi.
Maku ya yi watsi da tunanin da wasu ke yin a cewa sauke ministocin yana da alaka da siyasa. Ya ce: “Hatta kafafen watsa labarai sun yi ta kirdadon za a yi garambawul tuntuni.  Ba zan iya tunawa sau nawa a bara kafafen watsa labarai suna tunanin yiwuwar garambawul din. Hatta akwai wadanda suke rubutu balo-balo cewa suna son a yi garambawul ga majalisar. Kuma babu wata gwamnati a duniya da shugabanninta ba su yin garambawul ga majalisar ministocinsu. Babu! Kuma garambawul ga majalisar ministoci wani bangare ne na shugabanci. Na hakkake abin da Shugaban kasa ya yi abu ne mai sauki na sake sanya karsashi ga gwamnatinsa domin ta samu gagarumar nasara.”
Minista Maku ya kara da cewa Shugaban kasa yana da iko a kowane lokaci ya yi garambawul ga ministocinsa. Ganin damarsa ce a karkashin tsarin mulki, kuma hakan ba ya da alaka da wani dalili baya ga cewa gwamnatinsa ta cika shekara biyu, yana kokarin sake wa gwamnatinsa alkibla don sanya sababbin jini domin samun gagarumar nasarar yi wa jama’ar Najeriya aiki. Wannan shi ne kawai dalilin.”
Saukakken Ministan Tsare-Tsare Shamsudden Usman, bai halarci zaman majalisar ba, yayin da Ministar Muhalli Hajiya Hadiza Mailafiya ce ta yi ta maza ta yi wa manema labarai na fadar Shugaban kasa bayani bayan kammala taron.
Hajiya Malaifiya tag ode wa Shugaba Jonathan kan damar da ya ba ta na bauta wa kasa, inda ta ce: “Na kasance wani bangare na gwamnatin. Kuma tana bi na bashi. An girmama me ta kiranmu mu yi wa kasa aiki kuma za mu bar ta cikin girma da arziki, ina jin wannan shi ne abu mai muhimmanci. Rayuwar kuma za ta ci gaba. Da dama sun zo amma sun bar gwamnatin ba girma.
Game da ko korar ta girgiza ta, sai ta ce: “A’a. Duk mai hankali ya san rayuwa juyi-juyi ce, dole wata rana ka koma inda ka fito. Ko ba haka ba ne? A kowace Laraba na zo nan nakan zo da tunanin wata rana za a yi garambawul. Kuma ina godiya ga kowa da kowa. Na ji dadin aiki da ku dukka. Kuma ina rokon ku ba shirye-shiryen gwamnati goyon baya, musamman shirin Koriyar Babbar Katanga don yaki da hamada da sabuwar taswira da sauransu.”

…Gwamnan Jihar Kaduna ya rushe majalisar zartarwarsa

Daga Mohammad Yaba, Kaduna

A sherkarnjiya Laraba Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Mukhtar Ramalan Yero ya bi sawun Shugaban kasa wajen garambawul ga Majalisar Zartarawarsa inda ya kori daukacin kwamishinoninsa.
Wata sanarwa dauke da sa hannun Kakakin Gwamnan Jihar Malam Ahmed Maiyaki ya ce Gwamnan ya gode korarrun kwamishinonin bisa goyon baya da suka ba gwamnatinsa tare da kuma yi musu fatan alheri.
Sanarwar ta kuma umurci dukkan kwamishinonin su mika ragamar mulkin ma’aikatunsu ga manyan sakatarorin ma’aikatun a yau Juma’a 13 ga Satumba, 2013.
Wannan kora da Gwamnan ya yi ya zo ne sa’o’i kadan bayan Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ba da korar ministocinsa tara ciki har da wata minista daga Jihar Kaduna.