✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jonathan ya nemi a kara wa’adin dokar ta-baci a jihohin Arewa maso Gabas

Shugaban kasar Dokta Goodluck Jonathan ya nemi izinin Majalisar Dokoki ta kasa kan ta amince da karin wa’adin dokar ta-baci a jihohi uku da ke…

Shugaban kasar Dokta Goodluck Jonathan ya nemi izinin Majalisar Dokoki ta kasa kan ta amince da karin wa’adin dokar ta-baci a jihohi uku da ke Arewa maso Gabas da ke fama da hare-haren ’yan Boko Haram.

Shugaba Jonathan ya bukaci haka ne cikin wata wasika da ya aike wa Majalisar Dattawa da ta Tarayya a shekaranjiya Laraba, inda ya bukaci a kara tsawon wa’adin dokar wadda za ta kare aiki a wannan wata.
Shugaba Jonathan ya ce jami’an tsaro sun samu gagarumar nasara a wata shida na farko na dokar, kuma yana da yakinin zaman lafiya zai dawo a yankin da ke fama da rikici nan da wata shida masu zuwa.
Idan majalisun biyu sun amince da karin dokar za ta fara aiki daga ranar 12 ga Nuwamban nan. Wasikar Jonathan ta je Majalisar Dattawa ne a daidai lokacin da majalisar ta karbi rahoton kwamitinta da ya binciki kisan Apo da jami’an tsaro suka yi ga wasu masu kwana a wani gida da ba a kammala ba.
Sojoji da jami’an SSS sun yi da’awar cewa wadanda suka kashen ’yan Boko Haram ne, yayin da shaidu suka ce kisan gilla ne, kuma mahukunta sun kasa gabatar da shaidar da za ta tabbatar da da’awar tasu.
Jam’iyyun adawa da suka dunkule a Jam’iyyar APC sun nuna adawa da dokar a karon farko, sai dai ba a sani ba ko majalisun biyu za su amince da bukatar musamman sakamakon yadda ake zargun sojoji da wuce gona da iri wajen kashe fararen hulan da ba su san hawa ko sauka ba.
Ranar 14 ga Mayun bana ne Shugaban ya kafa dokar ta-baci a jihohin Yobe da Adamawa da Borno cibiyar kungiyar Jama’atu Ahlis Sunna Lid Da’awati wal Jihad da ake kira Boko Haram da mayakanta suka kashe daruruwan jami’an tsaro da fararen hula.
Dubban sojoji da ’yan sandan da aka kai yankin sun kora mayakan kungiyar daga cikin manyan birane amma ba su kai ga murkushe su dungurungum ba.