✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jonathan ya rika ziyartar kasashen makwabta maimakon sarakuna – Bala Jibrin

daya daga cikin kusoshin Jam’iyyar APC na kasa Kyaftin Muhammed Bala Jibrin, ya ce, ziyarar saduwa da shugabannin kasashen Kamaru da Chadi da Nijar domin…

daya daga cikin kusoshin Jam’iyyar APC na kasa Kyaftin Muhammed Bala Jibrin, ya ce, ziyarar saduwa da shugabannin kasashen Kamaru da Chadi da Nijar domin su taimaka wa Najeriya ta dakile matsalar ’yan Boko Haram ta fi muhimmanci fiye da ziyarar fadar sarakuna da Shugaba Goodluck Jonathan, ya yi a kwanan baya.
Kyaftin Bala Jibrin, wanda shi ne Mataimakin Mai binciken Kudi na Jam’iyyar APC ta kasa, ya fadi haka ne hirarsa da wakilinmu a Ibadan, inda ya ce, “Abin takaici ne yadda shugabanni suka manta da alkawarin da suka yi wa al’umma na kare rayuka da dukiyoyinsu, suka koma rububin neman mulki domin wasoson dukiyar. Idan ana son a yi gyara an san hanyoyin da za a gyara, amma saboda rashin tausayi an kyale miliyoyin talakawa cikin kunci abincin rayuwa, ba a taimaka musu a fannin aikin gona don su ciyar da kansu, an yi watsi da kula da kiwon lafiya da iliminsu sai rub da ciki ake yi da dubban biliyoyin Naira.”
Ya ce irin tabargazar da Jam’iyyar PDP ke yi a na kasa gudanar da mulkin jama’a ne ya jawo aka kafa Jam’iyyar APC da nufin gyara irin barnar da ake tafkawa. “Jama’ar kasar nan sun san mugun halin da PDP ta jefa su a ciki, shi ya sa suke neman canji kuma APC na da manufofin kyautata rayuwa da ci gaban al’umma,” inji shi.
 Kyaftin Bala ya ce, PDP ta kasa nuna wa jama’a ayyukan ci gaban da take cewa ta yi. Don haka ya bukaci talakwan kasar nan su tashi tsaye domin kawo canji da kuri’unsu a zaben gaba, “idan kuma suka yi zaben tumun dare to za su koma gidan jiya,” inji shi.