✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jose Mourinho ya yaba wa bictor Moses

Kocin kulob din Chelsea da ke Ingila Jose Mourinho ya nuna matukar farin cikinsa ganin yadda dan kwallon gabansa dan asalin Najeriya bictor Moses yake…

Victor MosesKocin kulob din Chelsea da ke Ingila Jose Mourinho ya nuna matukar farin cikinsa ganin yadda dan kwallon gabansa dan asalin Najeriya bictor Moses yake nuna kwazo a halin yanzu a kulob din.
Kocin ya bayyana haka ne a tattaunawa da ’yan jaridu jim kadan bayan kulob din ya lallasa na AC Milan a wasan sada zumunta a ranar Lahadin da ta gabata a Amurka.
Kocin ya bayyana farin cikinsa ganin yadda dan kwallon ne ya samu bugun fanariti a wasan su da kulob din Inter Milan da ke Italiya a makon jiya kafin ya taimaka taimaka wa dan kwallon Chelsea Andre Schurrle jefa kwallo ta biyu a ragar AC Milan da ke Italiya a ranar Lahadi a gasar sada zumunta da ta gudana a Amurka da hakan ta sa kulob din ya kai wasan karshe na cin kofin sada zumunta na ICC a tsakaninsa da kulob din Real Madrid.
“Na yaba da kwazon Moses musamman ganin yadda yake yi mana kokari a wannan lokaci sannan yana daya daga cikin ’yan kwallonmu da ba su taba yin lattin minti daya a sansanin da muke horar da su ba”.
“Moses na daga cikin ’yan kwallon da za mu yi alfahari da su a kakar wasa ta bana don haka ina shawartarsa da ya cigaba da zage damtse don ganin an dama da shi a wannan karon”, inji Mourinho.