✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Joseph Yobo ya zama Mataimakin Kocin Super Eagles

Hukumar Kwallon Najeriya, NFF ta zabi tsohon dan wasan Najeriya, kuma tsohon kyaftin din kasar, Joseph Yobo a matsayin Mataimakin Kocin ’yan kwallon Najeriya, wato…

Hukumar Kwallon Najeriya, NFF ta zabi tsohon dan wasan Najeriya, kuma tsohon kyaftin din kasar, Joseph Yobo a matsayin Mataimakin Kocin ’yan kwallon Najeriya, wato Super Eagles.

Yobo zai maye gurbin Imama Amapakabo a matsayin, inda zai ci gaba da aki tare da Gernot Rohr.

Tsohon dan wasan, ya buga wa kungiyoyi da dama a ciki da wajen Najeriya, ciki har da Everton, inda ya fi yin suna har ya kai ga zama kyaftin.

Ya buga Gasar Kofin Afirka sau 6, a shekarun 2002 da 2004 da 2006 da 2008 da 2010 da 2013.

Shi ne kyaftin din Super Eagles lokacin da Najeriya ta lashe Gasar Kofin Afirka a shekarar 2013.

A rukunin Super Eagles, Joseph Yobe ya bugawa Njeriya wasa 100. Ba ya ga wasannin da ya buga wa Najeriya a wasannin ’yan kasa da shekara 20.

A shekarar 2001 ne ya fara bugawa Super Eagles, inda ya taka leda a wasan Najeriya da Zambia a garin Chingola a watan Afrilun.

Ya kuma halarci Gasar Kofin Duniya sau uku, a shekarun 2002 da 2010 da 2014.