Search
Subscribe
Juyin juya-hali daga Allah babu hayaniya ba zubar da jini (2)

Juyin juya-hali daga Allah babu hayaniya ba zubar da jini (2)

Ina da yakinin wannan juyin juya-hali ya samu ne sakamakon yadda muka yarda cewa abubuwa sun tabarbare Najeriya tana bukatar komawa kan gwadabe na gaskiya, sakamakon kazamin satar da aka rika tafkawa a baya. Irin satar da ko gafiya wadda a duk dabbobin da Allah Ya halitta, babu mai raunin hankali irinta, ga shi dai tana da idanuwa da kunnuwa da kwakwalwa amma saboda dakikanci, idan ta zo wucewa, ta dunguri kafarka, ka haure ta ta gudu sai ta dimauce ta komo inda ka haure ta, Haka koda wutar lantarki mai tartsatsi ta dungura za ta iya komawa wurin, amma duk da haka, gafiya ta fi mafiya yawan shugabannin Najeriya hankali. Saboda na sha fadi cewa gafiya wani wuri take zuwa ta yiwo satar kayan abinci ta kai raminta wurin ’ya’yanta. Yayin da shugabannin Najeriya kasarsu suke yi wa sata karkaf, su kai wata kasar su boye. Idan aka tambaye su, me ya sa suke kaiwa wasu kasashe, sai su ce, kasashen da suka kai ajiyar dukiyar tamu da suka sace sun fi tsaro, Najeriya babu tsaro. Amma su da iyayensu da ’ya’yansu da matansu da duk wadanda suke kauna suna zaune a Najeriya! Wato dukiyar kasarmu da suke ta sacewa ta fi rayukansu muhimmanci. Bayan a matsayinsu na shugabanni su ne da alhakin samar da tsaron rayukan dukkan ’yan Najeriya da lafiyarsu da dukiyarsu da mutuncinsu da addininsu. Jami’an tsaro da kotuna da alkalai da ma’aikatan lafiya duk suna karkashinsu ne. 

Wadannan da gafiya ta fi su hankali su ne suke ganinmu mu da muka kori soja tamkar mu ba “hilun bi hazal balad” ba ne. Saboda raunanan da suke bauta musu suna ba su dan abin da bai taka kara ya karya ba daga dukiyarmu da suka sace.
Abin aunawa a nan shi ne yayin da gafiya ta fi shugabanninmu hankali, to, mu da muke zaben su, ko ake zaba mana, muke yarda kamar sun ci mu da yaki, wane irin hankali muke da shi? Irin dimokuradiyyar tamu ke nan? Arzikin kasa ba ya da amfani, hankali ba ya da amfani? Idan muna so a canja wannan, tilas ne kowannenmu sai ya canja halinsa, mu daina saba wa Allah, mu daina zaluntar juna.
Mu tuba tuba ta gaskiya ta hanyar yin nadamar miyagun ayyukan da muka yi ko muke yi da niyyar ba za mu kuma sakewa ba, mu tuna wutar munafuki tana karkashin ta Yahudu da Nasara da sauran kafirai. Allah ba zai canja mana ba sai mun canja, mu guji girman kai da hassada da algushu da tauye ma’auni, (sarakuna da malamai da ’yan kasuwa) gare ku. Mu yi adalci a kan kowa, mu daina kwadayi da tsoro da munafunci. Masu mulki da talakawa gare mu. Kamar yadda duk wata lalacewa ba ita ta yi kanta ba, wasu ne suka lalata, haka ma duk wani gyara ba zai yi kansa ba, har sai wasu sun hadu sun yi gyaran. Koda Annabawa (AS) sai da suka samu hadin kan wadanda ba Annabawa ba suka taimaka, Annabawan suka isar da sakon Allah. Idan har akwai imani, to, akwai rabo, idan hankali ya bata hankali ne ke nemo shi. Idan barayi suka yi sata, ba barayi ne suke kwatowa ba, masu kaya ne suke kwato su! Idan gobara ta taso ba sai da ruwan famfo za a kashe ta ba, komai kazantar ruwa idan zai kashe gobarar sai a yi amfani da shi, sai an kashe gobarar kurmus, a fara tunanin yin wankan tsarki, yadda za a guji faruwar wata gobarar nan gaba.
Wankan tsarki:
Tunda aka kashe su Sardaunan Sakkwato Sa Ahmadu Bello Firimiyan Jihar Arewa, har yanzu an kasa samun wadanda za su inganta noma da kiwo da jima da dukanci da saka da rini da kira da sassaka da fatauci. Kai hatta hukumomin gwamnati kamar hukumar sayen amfanin gona (Marketing Board) da kamfanin zuba jari na Arewa (NNDC) da sauran na tarayya duk an bar su kodai sun mace ko suna some. Gwamnonin Arewa sun sayar da Bankin Arewa ga wasu tsofaffin shugabanni ina kudin? Ba a maganar bankunan gama-kai. Tilas a binciki kowa tun daga sama har kasa a tabbatar da dukiyar da kowane shugaba ya mallaka da yadda ya same ta, a kwato duk abin da aka sace mana.
Abin da ke kan sababbin shugabannin kasar nan a yanzu shi ne su kaddamar da kwamiti mai karfin shari’a wanda zai bi kadin duk abin da kowane tsohon shugaba da ma’aikaci ya mallaka a ko’ina, a duniya, ya yi bayanin yadda ya same su, idan iyayensa ne suka mutu ya gada a bar masa, idan kuma satar mana ya yi, a kwato mana kayanmu! Duk rayukan da suka salwanta ba tare da shari’a ba a biya diyyarsu, a hukunta duk wani shugaba daidai da yadda Allah Ya yi umarni ayi, shi ne zaman lafiyarmu da matakin ci gabanmu da kasarmu. Ta yadda za a daina hallaka miliyoyin talakawa saboda daure wa azzaluman shugabanni gindi suna sace arzikin kasarmu, suna kaiwa wasu kasashe suna boyewa.
Wajibi ne mu hadu da shugabannin yanzu wajen kawar da kowace irin matsala ta kisa da sata da tsafi da fajirici, yadda za mu zama tsarkakkiyar al’umma masu imani da tsoron Allah.
Mu suffantu da hankali da adalci, yadda za mu kauce wa kowace annoba da wasu ke jawo wa dukkan al’umma, al’ummar Najeriya mu ji tsoron Allah mu tsarkake zukatanmu mu zama masu adalci a junanmu, yin haka shi ne kubutarmu a wurin Allah, Mai rayawa, Mai kashewa, Mai arzutawa, Mai talautawa, Mai bayar da mulki, Mai kwacewa, kuma Shi ne Madawwami.
Kowa zai mutu, babu wanda ya isa ya zabi irin mutuwar da zai yi, ko lokaci ko wurin da zai mutu. Babu wanda za a binne da Naira ko Dala ko Fam ko Riyal. Komai yawan dukiyar da ya tara koda ta halal ce balle ta haram.
daiyabu, Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya,
(Mobement for Justice in Nigeria – MOJIN),Kano. 08023106666, 08060116666

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin