✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ka kira taron shagabannin jam’iyya ko ka ajiye aiki – Gwamnonin APC ga Oshiomhole

Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC sun nuna rashin jin dadinsu kan rikicin da ke cin jam’iyyar, inda suka bukaci Shugaban Jam’iyyar ta Kasa, Kwamred Adams Oshiomhole…

Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC sun nuna rashin jin dadinsu kan rikicin da ke cin jam’iyyar, inda suka bukaci Shugaban Jam’iyyar ta Kasa, Kwamred Adams Oshiomhole ya shirya taron shugabannin jam’iyyar da gaggawa ko ya sauka daga kujerarsa.

Kungiyar Gwamnnonin APC din ta bada wannan sanarwar ce sakamakon rikicin siyasar da ke tsakanin Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki da Kwamared Oshiomhole da sauran rikice-rikicen da jam’iyyar ke fama da su a fadin kasar nan. Ta yi tambayoyin cewa: “Mene ne dalilin da ya hana taron shugabannin jam’iyya ko kuma taron jam’iyya wanda ya kamata a yi duk wata hudu? A kan me wadansu sassan jam’iyyar a karkashin mulkin Oshiomhole za su ci gaba da fuskantar irin wadannan matsalolin?”

Kungiyar Gwamnonin APC ta sake tambayoyi cewa, “Mene ne Oshiomhole ke fatar cimmawa a matsayin Shugaban Jam’iyyar ta Kasa? Shin akwai wani yunkurin da yake yi ne don habaka jam’iyyar? A yayin da akwai bukatar taron shugabannin jam’iyyar, gwamnoni sun ce: “A halin da ake ciki yanzu, babu abin da zai shawo kan matsalar nan da ta wuce taron shugabannin jam’iyyar. Ko Oshiomhole ya mutunta kundin tsarin mulkin jam’iyyar, kuma ya kira taro don shawo kan kalubalen da jam’iyyar ke fuskanta ko kuma ya rungumi cewa ba zai iya tafi da al’amuran jam’iyyar ba, ya ajiye aiki, dole ne mu ga an kawo karshen kalubalen da jam’iyyarmu ke fuskanta,” inji takardar.